Bello Jibrin Gada

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bello Jibrin Gada
Minister of Culture and Tourism (en) Fassara

17 Disamba 2008 - 17 ga Maris, 2010
Adetokunbo Kayode - Abubakar Sadiq Mohammed
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 -
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Mayu 1999 - 2003
District: Sokoto East
Rayuwa
Haihuwa jihar Sokoto, 1954 (69/70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Bayero
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Nigeria Peoples Party

Bello Jibrin Gada dan siyasan Najeriya ne wanda ya taba zama Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas daga watan Mayun shekarar 1999 zuwa watan Mayu shekarar 2003. An nada shi Ministan Al'adu da Yawon Bude Ido a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2008 bayan da Shugaba Umaru 'Yar'Adua ya yi wa majalisar ministoci garambawul. Ya bar ofis a watan Maris na shekarar 2010 lokacin da Mukaddashin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An kuma haifi Gada a shekarar 1954. Ya halarci Jami’ar Bayero ta Kano da kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. An kuma zaɓe shi Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a karkashin jam'iyyar All Nigeria People Party (ANPP), yana rike da mukami daga watan Mayu shekarar 1999 zuwa watan Mayu shekarar 2003. Ya kuma yi aiki a matsayin Mai Yaran Marasa Rinjaye a lokacin da yake kan karagar mulki. Bayan haka, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, inda kuma ya zama shugaban jam'iyyar ta Democratic Party ta jihar Sokoto.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Nigeriafirst Ng. "Bello Jibrin Gada". Archived from the original on 2010-10-29. Retrieved 2021-02-20. Cite has empty unknown parameter: |4= (help)CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)