Abubakar Sadiq Mohammed
Appearance
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Nafada, 14 Oktoba 1961 (64 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Harshen uwa | Hausa | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Jami'ar Maiduguri Jami'ar Ibadan | ||
| Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da minista | ||
An naɗa Abubakar Sadiq Mohammed a matsayin ministan yawon bude ido, al'adu da wayar da kan kasa a ranar 6 ga Afrilun 2010, lokacin da Muƙaddashin Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya sanar da sabuwar majalisar ministocinsa.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Ya sami B.Sc (Physics) a 1985 daga Jami'ar Maiduguri da kuma M.Sc (Physics) daga Jami'ar Ibadan. Malami ne a Jami’ar Fasaha ta Tarayya Yola (1986–1996). Ya kasance Manajan Darakta ko Shugaba na kamfanoni da yawa tsakanin 1996 da 2002. Ya yi aiki a Cibiyar Malamai ta Kasa, Kaduna (2002-2008). A shekarar 2008 ya zama Shugaban Ma’aikata na Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Bayero Nafada.