Bello Maitama Yusuf

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bello Maitama Yusuf
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 - Mujitaba Mohammed Mallam
Rayuwa
Haihuwa Jihar Jigawa, 14 ga Afirilu, 1947
ƙasa Najeriya
Mutuwa jihar Kano, 13 Oktoba 2023
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Jam'iyyar National Party of Nigeria
All Nigeria Peoples Party (en) Fassara

Bello Maitama Yusuf Sardaunan Dutse, an haife shi a watan Afrilu, na shekara ta 1947 ya rasu a watan octoba a shekara ta 2023 (1947-2023) ya mutu yanada shekara 76, ya kasan ce ɗan siyasan Nijeriya ne, ɗan Kasuwa kuma Sanatan Tarayyar Najeriya. Ya kasance Ministan Harkokin Cikin Gida a shekara ta 1979 da Ministan Kasuwanci a shekara ta 1982. Ya yi karatu a Jami'ar kofar arewa\ Washington kuma ya kasance memba na rusasshiyar National Party of Nigeria. Kafin ya shiga siyasa, ya kasance lauya kuma ɗan kasuwa kuma ya yi aiki a matsayin babban mai rejista a Kotun Majistare ta Kano. Ya kuma kasance memba na majalisar tsarin mulki kuma yana daya daga cikin 'yan biliyan Jigawas har zuwa yanzu. Bello Maitama ya kafa fage ga duk ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa a Najeriya. [1] A matsayin sa na Ministan Kasuwanci, ya kasance mai kula da takaita shigo da kaya zuwa Najeriyar wanda hakan ke matukar lalata asusun kasar na kasashen waje .

An zabe shi zuwa majalisar dattijan Najeriya mai wakiltar mazabar Jigawa ta Kudu maso Yamma a watan Afrilun shekara ta 1999, sannan ya sake zuwa a watan Afrilun shekara ta 2003. Ya taka muhimmiyar rawa wajen kai hare-hare kan Ka'idoji na Uku da kuma tuhumar Shugaba Obasanjo da barnatar da asusun bunkasa man fetur, ya kuma kasance sanannen memba na kwamitin Majalisar Dattawa kan matasa da wasanni.[ana buƙatar hujja] An kuma bashi mukamin "Sarduanan Dutse" a jiharsa wato jihar Jigawa. Bello Maitama a yanzu ya yi ritaya daga siyasa da kasuwanci, inda babban ɗan sa Yusuf ya ci gaba da gadon sa.

Bayanan kula[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Nigerian President's Visit to Romania," British Broadcasting Corporation, September 18, 1982