Ben Diogaye Bèye
Ben Diogaye Bèye | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Senegal da Dakar, 1947 (76/77 shekaru) |
ƙasa | Senegal |
Karatu | |
Harsuna |
Faransanci Yare |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida, darakta, marubin wasannin kwaykwayo da mai tsarawa |
IMDb | nm0079884 |
Ben Diogaye Bèye (an haife shi a shekara ta 1947) marubucin fina-finai ne na Senegal, mai shirya Fina-finai, kuma ɗan jarida. Ya kasance mataimakin darektan kusan fina-finai goma sha biyu na Senegal, ciki har da Touki Bouki tare da Djibril Diop Mambety, Baks tare da Momar Thiam, Sarah da Marjama tare da Axel Lohman.[1]
Ya yi karatu a birnin Paris, ya kasance ɗan koyo ga sanannun masu shirya fina-finai na Senegal, ciki har da Ousmane Sembène, Ababacar Samb, da Djibril Diop Mambety. Haka-zalika ya kasance mai watsa shirye-shiryen rediyo na Rediyon Senegal kuma a matsayin ƙwararren ɗan jarida, yana jagorantar sashen "Sports and Culture" na kamfanin dillancin labarai na Senegal.
Fim ɗinsa farko (gajeren fim) shi ne Les Princes Noirs de Saint Germain-des-Près, wanda aka saki a shekarar 1972, wanda kuma shine mafi kyawun fim nasa da aka sani. Yana bayar da labarin a kan wani matashi da ba shi da aikin yi na Afirka yana ƙoƙarin rayuwa daban a babban birnin Faransa. [1] An saki fim dinsa na biyu, Samba Tali, a farkon shekara ta 1975. [1] Ya samar kuma ya ba da umarni bisa ga rubutu fim ɗin da kansa. [1] Ya sami Kyautar Kyautattun Fim a Bikin Fim na Duniya na Ensemble Francophone a Genèva a 1975 da kuma a Bikin Carthage a 1976.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 "Bèye Ben Diogaye – Sénégal". Africultures (in French). 2007-10-20. Archived from the original on 2013-01-02. Retrieved 2008-09-16.CS1 maint: unrecognized language (link)