Jump to content

Beth Mead

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Beth Mead
Rayuwa
Haihuwa Whitby (en) Fassara, 9 Mayu 1995 (29 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Karatu
Makaranta Teesside University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Sunderland A.F.C. Women (en) Fassara2011-2017
Arsenal W.F.C. (en) Fassara2017-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Tsayi 1.63 m
hoton yar kwallo beth mead
hoton beth mead

Bethany Jane Mead (an haife ta a 9 May shekarar alif dari tara da casa'in da biyar miladiyya 1995) ta kasance shahararriyar 'yar wasan kwallon kafar kasar Ingila, wadda take buga wasan gaba a Kungiyar FA WSL na kulub din Arsenal da kuma a Kungiyar kwallon kafar England ta mata.

Matakin kulub

[gyara sashe | gyara masomin]
Beth Mead

Mead ta fara wasan samartakar ta ne a California Girls FC kafin ta koma kulub din Middlesbrough F.C. A lokacin tana da shekara 10, sannan a shekarar da ta cika 16 ta koma kulub din Sunderland, a gasar FA Women's Premier League A kakarta ta farko a Kungiyar ta samu cin kwallaye 23 a dukkanin wasannin da ta buga a gasar, kuma ta Kare kakar ne da kwallaye 29 a dukkanin gasanni. Sannan a kakar da ta biyo baya ta ci kwallaye 30 a wasanni 28, inda ƙwallaye 15 a cikin gasar 2014 FA WSL inda ta taimaka wa kulub din Sunderland kaiwa ga gasar WSL 1. Duk da cewa Mead ta zama shahararriyar 'yar wasa bayan cigaba da kulub din Sunderland ta samu, sai ta fita don ta koma makaranta ta kammala shekaran karshenta ta jami'a. Sannan kuma ta amince da ta yi aiki a matsayin barmaid a wani pub dake garin da take, lokacin da take hutu, don nuna godiya ga masu wurin, wadanda sun taimake ta da tallafin kudin da ta samu ta fara wasa.[1]

A wasan ta na farko a babban rukunin gasar, Mead ta ci kwallon wa Sunderland a wasan da Kulub ta ci 2–1 Liverpool wanda su ne masu rike nasarar fitattun zakaru.[2] A ranar 19 ga watan Yuli, 2015, Mead ta ci kwallaye uku hat-trick a wasanta da kungiyar Chelsea wadanda su ne a saman tebur, inda ta zama mafi yawan kwallaye da kwallon takwas.[3] A cikin makon, Mead ta tsallake hatsari bayan motar ta ta yi juyi har uku sanadiyar kokarin da ta yi na kauce wa wata barewa.[4] A kuma makon da ya biyo baya, Mead ta ci kwallaye biyu a wasan da suka yi nasara 4–1 da Bristol, sai kungiyar ta ta Sunderland ta haye saman tebur din WSL 1.[5] Ta Kare kakar 2015 na gasar WSL1 da kwallaye 12 a wasanni 14 kuma mafi yawan kwallaye a gasar.[6]

Beth Mead a Arsenal shekara ta 2018.

A ranar 24 ga watan Janairu, 2017, an bayyana Matan Arsenal da cewa sun sayi Mead akan wasu kuɗi da ba a bayyana ba.[7]

  1. "Mead eager to revise Canadian experience". FIFA. 19 January 2015. Archived from the original on 6 July 2015. Retrieved 2 July 2019.
  2. "Exclusive: Beth Mead". Shoot (football magazine). 23 April 2015. Archived from the original on 20 May 2015. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)
  3. Currie, Jo (19 July 2015). "Carlton Fairweather: Beth Mead 'deserves' senior England call". BBC Sport.
  4. Currie, Jo (18 July 2015). "WSL 1: Sunderland Ladies 4–0 Chelsea Ladies". BBC Sport. Retrieved 19 July 2015.
  5. "Williams says Sunderland's sights are set on the top". FA WSL. 25 July 2015.
  6. Stillman, Tim. "Arseblog Exclusive- Interview with Arsenal Women Striker Beth Mead | Arseblog News – the Arsenal news site" (in Turanci).
  7. "Beth Mead: Arsenal Ladies sign Sunderland striker ahead of WSL Spring Series". BBC Sport (in Turanci). 2017-01-24. Retrieved 2017-01-24.