Bilala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bilala
mutane
Bayanai
Harsuna Harshen Naba
Addini Musulunci
Ƙasa Cadi

Bilala mutane ne musulmai da ke zaune a kusa da tafkin Fitri, a cikin yankin Batha, a tsakiyar Chadi. A karshe C ƙidayan da kasar chadi tayi a acikin shekarar 1993 ya bayyana cewa, sun ƙidaya 136.629 mutane yan yaren Bilala sun kuma samu harsuna masu nasaba, da yaran har kashi huɗu, kuma yana cikin rukunin Nilo-Saharan ; biyu daga cikin makwabta ne sune, Kuka da Medogo . Wadannan ukun kuma su ne suka hada yaran Lisi kuma ana tinanin cewa su tsatsan kabilun Sultanate ne da kuma Yao .

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

Sun fara bayyana ne a cikin karni na 14th a kusa da tafkin Fitri matsayin kabila mai jagorancin na daular Sayfawa. Asalinsu wani yanki ne na siyasa wadanda suka gudo a sakamakon tsanantawa daga kabilar Kayi (tsohuwar Zaghawa = Kanembu na yanzu, dangin sun kasance har yau a Kanem) da kuma dangin Ngizimis Kanembu wanda har yau suke a Dibbinintchi, Tsibirin Tchad mazaunan yanki Fittri. [1] Sun zauna ne a gabas a Daular borno, wanda a yau Chadi ce, sun rafke karfin daular kanem da ikon ta, inda suka kashe biyar ko kuma shida daga cikin mais (sarakuna) Daular a tatsakanin 1376 da kuma 1400.

A karshe dai Bulala sun ci nasarar mamaye Daular kanem da kuma tilasta ma mais (sarakuna) da suyi ƙaura zuwa Borno . Sakamakon haka, Bulala sun samu madafun iko a kan Kanem, wanda aka kafa a ƙarni na 15 na sarkin Musulmi na Yao. daga baya Masarautar Kanem-Bornu ta kai hari bayan wani karni a karkashin mulkin Ali Gaji. Yaran Ali ya kwato Kanem bayan gwabzawar yaki a Garni kiyala, wanda ya tilastawa Bulala ƙaura zuwa gabas, inda zasu ci gaba da kasancewa a cikin haɗari har izuwa ƙarni na gaba Kanem-Bornu ta cigaba da kasancewa masarauta mai haɓaka: wani matafiyi mai suna Leo Africanus yace mulkin Bulala ya fi mulkin Kanem-Bornu arziki a cinikayya da samu a huldar su da ƙasar Masar .

karfin su ya ci gaba ne har izuwa farkon mulkin mallaka, lokacin da suka miƙa kai ga Faransawa .

Diddigin bayanai[gyara sashe | gyara masomin]

  1. ^ H. R. Palmer "History of the first twelve years of the reign of Mai Idris Alooma of Bornu (1571-1583), by his Imam Ahmed Bin Furtua"