Bola Afonja
Appearance
Bola Afonja | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Oyo, 21 ga Faburairu, 1943 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Mutuwa | 19 Mayu 2024 |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Nigeria Peoples Party |
Bola Afonja (an haife shi 21 ga watan Fabrairun 1943 kuma ya mutu a ranar 20 ga Mayu, 2024) ɗan siyasar Najeriya ne. Ya taɓa zama ministan ƙwadago a ƙarƙashin Ernest Shonekan,[1] kuma ya taɓa zama memba a kwamitin amintattu na jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).[2]
Ya kasance shugaban kwamitin gudanarwa na bankin First Bank plc, babban bankin kasuwanci a Najeriya. Ya yi ritaya daga hukumar bayan cikarsa shekaru 70 a ranar 21 ga watan Fabrairun 2013.