Jump to content

Bolaji Ayinla

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bolaji Ayinla
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
District: Mushin II
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 -
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 10 Oktoba 1959 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Bolaji Yusuf Ayinla (wanda aka fi sani da B.Y.A) ɗan siyasan Nijeriya ne kuma ɗan Majalisar Wakilai ta Nijeriya mai wakiltar Mazabar Mushin II ta Tarayya bayan da ya yi nasara a babban zaɓen Nijeriya na 2015 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressive Congress.

Rayuwar Farko da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Bolaji Ayinla an haife shi a 1960 a Lagos, Najeriya. Ya halarci makarantar sakandaren musulmai, Sagamu, jihar Ogun inda ya samu takardar shedar kammala makarantar sakandaren yammacin Afirka. Ya ci gaba zuwa Cibiyar Nazarin Kasuwanci da Gudanarwa don samun takardar difloma.

Harkar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bolaji Ayinla ya fara siyasarsa ne a 2003 bayan an zabe shi ya wakilci mazabarsa a majalisar dokokin jihar Legas daga 2003 zuwa 2015 a karkashin inuwar kungiyar Action Congress of Nigeria. Ya tsaya takarar dan majalisar wakilai ta tarayya a karkashin dandamalin All Progressive Congress kuma ya samu wakilcin mazabar Mushin II ta Tarayya a babban zaben 2015 na Najeriya.

https://www.nassnig.org/mps/single/195 Archived 2020-12-03 at the Wayback Machine

https://www.medianigeria.com/biography-of-bolaji-ayinla/ Archived 2021-10-30 at the Wayback Machine

https://theexplicitnews.wordpress.com/2018/12/18/hon-bya-bolaji-yusuf-ayinla-the-records-the-precedents-the-biography-and-the-next-level/

http://encomium.ng/my-victory-is-god-hard-work-and-sincerity-hon-bolaji-yusuf-ayinla/