Jump to content

Cara Mund

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Cara Mund
Rayuwa
Haihuwa Bismarck (en) Fassara, 8 Disamba 1994 (29 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Ƴan uwa
Ƴan uwa
Karatu
Makaranta Jami'ar Brown
Century High School (en) Fassara
Harvard Law School (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai gasan kyau
IMDb nm9267012

Cara D. Mund (/ˈkɑːrə/ KAR-ə; an haife ta a ranar 8 ga watan Disamba, shekara ta 1993) [1] [2] lauya ce 'yar Amurka kuma tsohuwar wacce ta lashe lambar yabo daga Bismarck, Arewacin Dakota. A watan Yunin 2017, an naɗa ta Miss North Dakota 2017. A ranar 10 ga Satumba, 2017, an naɗa ta Miss America 2018 a Birnin Atlantic kuma ta kasance 'yar takara ta farko daga Arewacin Dakota da ta lashe wannan gasar.

Kuruciya da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mund a Bismarck, Arewacin Dakota ga iyaye DeLora Kautzmann-Mund kuma Doug Mund.[3]

Mund mai tsara wasan kwaikwayo ce kuma 'yar rawa.[4] A makarantar sakandare, ta horar na tsawon bazara hudu tare da Gidan Rediyon Birmim Rockettes kuma an kira ta da daya daga cikin "Mata masu nasara na Rockette" a shekara ta 2019. [5][6] Tun tana 'yar shekaru 14, Mund ta shirya taron baje kolin kayan ado na shekara-shekara wanda ke amfana da Gidauniyar Make-a-Wish . [2] A makarantar sakandare, Mund ta yi aiki a matsayin shugabar kungiyar girmamawa ta kasa, ta kammala karatu a matsayin daya daga cikin zakarun ajinta, kuma an zabe ta "wacce ta fi cancanta ta zamo Miss America".

Mund a cikin Atlantic City bayan an naɗa ta Miss America 2018

Ta kammala karatu tare da girmamawa daga Jami'ar Brown a 2016 da digiri a harkokin kasuwanci, sana'oi, da masana'antu. Binciken ta ya kasance a kan kungiyar Miss America. [7] Mund ta yi aiki a matsayin shugaban ƙungiyar Kappa Delta. [8] Ta ce makarantar ta taimaka mata "yi tunanin ƙafafunta".[kanta][1][7]

Daga watan Agusta zuwa Disamban shekara ta 2016, ta yi aiki a matsayin Sanata na Jamhuriyar Republican John Hoeven. [9]

A shekara ta 2019, Majalisar Wakilai ta Arewacin Dakota ta zartar da ƙuduri No. 3035 don karrama Mund.[10] An kuma shigar da ita cikin littafin Bluebook na Arewacin Dakota "Fitattun Arewacin Dakotans" kuma an san ta a matsayin ɗaya daga cikin "Mata biyar da suka canza Tarihin Arewacin Dakota. " A ranar 11 ga Maris, 2021, Gidan Tarihin Jihar North Dakota ta gabatar da nune-nunen da ke gabatar da Mund. [8][11]

Kafin a naɗa ta Miss America, ta bayyana shirin ta na halartar makarantar sharia.[2] A watan Mayu na shekara ta 2022, Mund ta kammala karatu daga Harvard Law School Cum Laude inda ta kasance karamar malama, Babban Edita na Mujallar Harkokin Wasanni na Jami;ar Harvard Shari'ar Nishadi, memba na Kungiyar Law School Mock Trial na Jami'ar Harvard, kuma memba ce ta Kungiyar Shari'ar Mata.[12][13][14] A ranar 23 ga Satumba, 2022, an rantsar da Mund kuma an shigar da ita aiki a matsayin lauya a Arewacin Dakota. [15][16]

Wasanni[gyara sashe | gyara masomin]

Farkon Wasanni[gyara sashe | gyara masomin]

Ta fara wasan nuni na ado tun tana yarinya, ta kuma samu lambobin yabo na Karamar Sarauniyar Kyau ta Arewacin Dakota, Sarauniyar Kyau Kwaila ta Arewacin Dakota, da Kuma Sarauniyar Kyau Budurwa ta Arewacin Dakota. [17] Mund daga baya ta yi gasa a gasar Sarauniyar Kyau Budurwa mafi Fice ta Arewacin Dakota 2010 a matsayin Miss Red River Valley's Outstand Teen. Ta ci gaba da lashe gasar, kuma ta shiga gasar Miss America's Outstanding Teen 2011. [2] Daga baya ta zamo ta 4 a matsayi na biyu a gasar Sarauniyar Kyau Budurwa ta USA 2012. [18]

Sarauniyar Kyau ta Arewacin Dakota[gyara sashe | gyara masomin]

Ziyarar USO ta Mund

Mund ta yi gasa a Sarauniyar Kyau ta Arewacin Dakota 2016 a matsayin Miss Oil Country, kuma ita ce ta biyu. Ta koma gasar a shekara mai zuwa a matsayin Miss Northern Lights 2017, kuma an naɗa ta Sarauniyar Kyau ta Arewacin Dakota 2017, tare da taken ta "A Make-A-Wish Passion with Fashion".[3]

Saruniyar Kyau ta Amurka 2018[gyara sashe | gyara masomin]

Mund ta wakilci Arewacin Dakota a gasan Sarauniyar kyau ta Amurka na 2018, gasar da aka gudanar a dakin taro na Boardwalk Hall a Birnin Atlantic, New Jersey, a cikin watan Satumban 2017. Sunanta na dandali shine "A Make-A-Wish Passion with Fashion." A gasar farawa, an nada Mund a matsayin ta biyu da kyautar Lamban Yabo ta Ingancin Rayuwa.[19]

Bayanan da aka ambata[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Happy 17th Birthday, Cara Mund". Bismarck Tribune. 5 December 2010.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "Bismarck's Cara Mund crowned Miss North Dakota". Grand Forks Herald. June 12, 2017. Retrieved September 10, 2017.
  3. 3.0 3.1 "Miss North Dakota". Miss America Organization. Archived from the original on September 10, 2017. Retrieved September 10, 2017.
  4. Gore, Leada (2017-09-11). "Miss America 2018: Miss North Dakota wins the crown". al.com (in Turanci). Retrieved 2019-03-13.
  5. "Miss America 2018 is an Alumni[sic] of the Rockettes Summer Intensive". The Rockettes (in Turanci). 14 September 2017. Archived from the original on 2020-09-25. Retrieved 2019-03-13.
  6. "Women's History Month: Celebrating Successful Rockette Women". The Rockettes (in Turanci). Retrieved 2019-03-13.[permanent dead link]
  7. 7.0 7.1 Sloan, Louise (March–April 2018). "Miss America, Feminist". Brown Alumni Monthly. www.brownalumnimagazine.com.
  8. 8.0 8.1 "Cara Mund". Linkedin.com. Retrieved September 14, 2017.
  9. Dalrymple, Amy (September 12, 2017). "Mund proud to put North Dakota 'on the map' as state's first Miss America".
  10. "House Concurrent Resolution No. 3035" (PDF).
  11. "ND style fashion exhibition opens in ND Heritage Center & State Museum". minotdailynews.com (in Turanci). Retrieved 2022-01-11.
  12. "JSEL Leadership" (in Turanci). Retrieved 2022-01-11.
  13. "Previous Members – Harvard Law School Mock Trial Association" (in Turanci). Archived from the original on 2022-01-11. Retrieved 2022-01-11.
  14. Simon, Clea. "'I was able to feel like I was making an impact'". Harvard Law Today (in Turanci). Retrieved 2022-07-28.
  15. "North Dakota Court System - 37 new lawyers admitted to N.D. bar". www.ndcourts.gov. Retrieved 2022-09-28.
  16. "North Dakota Court System". www.ndcourts.gov. Retrieved 2022-09-28.
  17. Feldman, Kate (September 10, 2017). "Miss North Dakota, Cara Mund, wins Miss America 2018".
  18. "Miss North Dakota USA & Teen USA state pageant results". Pageant Update Results. Archived from the original on 2022-10-05. Retrieved 2018-10-02.
  19. Morgan, Ike (September 8, 2017). "Miss Alabama Jessica Procter wins Miss America Quality of Life Award". AL.com. Retrieved September 10, 2017.

Haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

Awards and achievements
Magabata
{{{before}}}
Miss North Dakota Magaji
{{{after}}}
Magabata
{{{before}}}
Miss America Magaji
{{{after}}}

Samfuri:MissAmericas 2000–2019Samfuri:Miss AmericaSamfuri:North Dakota pageant winners