Charles Quaker-Dokubo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Charles Quaker-Dokubo
Rayuwa
Haihuwa 23 ga Maris, 1952
Mutuwa 25 ga Augusta, 2022
Sana'a
Sana'a Malami

Charles Quaker Dokubo malami ne ɗan Najeriya kuma tsohon mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan Neja Delta kuma kodinetan shirin afuwa na shugaban kasa (PAP).[1][2][3]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Charles Quaker Dokubo a ranar 23 ga watan Maris, 1952, a Abonnema, ƙaramar hukumar Akuku Toru, jihar Ribas.[4]

Dukkanin karatunsa na firamare da sakandare ya gudana ne a garin Abonnema kafin ya tafi Burtaniya da halartar Kwalejin fasaha ta Huddersfield da ke Yammacin Yorkshire don kammala matakinsa na "A".

Bayan ya sami digirin digirgir a fannin tarihi da siyasa na zamani daga jami'ar Teesside da ke Middlesbrough, Dokubo ya ci gaba da samun digiri na biyu a fannin nazarin zaman lafiya da kuma PhD a kan yaɗuwar makaman nukiliya da sarrafa shi daga jami'ar Bradford a shekara ta 1985.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Dokubo Farfesa ne na Bincike a Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa ta Najeriya da ke Legas, Najeriya kafin a naɗa shi mai kula da shirin afuwa na shugaban kasa (PAP) a shekarar 2018.[5]

Ya kasance mai kula da rajistar masu kaɗa kuri’a a lokacin zaɓuka na musamman na shekarar 1997 a Laberiya a matsayin memba na kungiyar taimakon fasaha ta kungiyar kasashen yammacin Afirka.[6]


A shekarar 2020 ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da shi bayan zargin almundahana da dukiyar ƙasa.[7][3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Akekegha, Igho (14 July 2019). "Dokubo: Niger Delta needs to take good advantage of opportunities we are given". The Guardian (Nigeria).
  2. Onukwugha, Anayo (25 August 2022). "Ex-Presidential Amnesty Boss, Dokubo, is Dead". Leadership News.
  3. 3.0 3.1 "Why Buhari suspend coordinator of presidential amnesty programme". BBC News Pidgin. 2020-02-29. Retrieved 2022-08-31.
  4. Akinwale, Yekeen (March 14, 2018). "New head for amnesty programme as Buhari launches probe into 'financial impropriety'" (in Turanci). International Centre for Investigative Reporting. Retrieved 2022-08-25.
  5. "Professor Charles Quaker Dokubo Archives". City People Magazine (in Turanci). Retrieved 2022-08-25.
  6. "Charles Quaker-Dokubo". Africa Portal. Retrieved 2022-08-26.
  7. Ailemen, Tony (February 29, 2020). "Buhari approves suspension of Charles Dokubo". Business Day. Retrieved 2022-08-25.