Chitchat on the Nile
Chitchat on the Nile ( Larabci: ثرثرة فوق النيل ( Adrift on the Nile ) wani fim ne na shekarar 1971 wanda ya dogara da littafin shekarar alif 1966 Adrift on the Nile na Marigayi Naguib Mahfouz mai lambar yabo ta Nobel. Fim ɗin memba ne a cikin jerin fina-finan Masar na Top 100.
Lokacin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Fim ɗin ya fito ne a zamanin gwamnatin Anwar Al Sadat kuma cikin gaggawa aka cire shi daga kasuwa saboda ana kallon fim ɗin a matsayin sukar zamanin Nasser, inda ake yawan danne fina-finan da ba su dace da siyasar Nasser da akidarsa ba. Anwar al-Sadat bai so ya bata wa al'ummar kasar Masar rai ba, waɗanda har yanzu wasunsu suna ƙaunar Nasser kuma suna girmama su.
Fina-finan sun yi magana ne a zahiri game da batun shan muggan kwayoyi, da kuma lalatar da aka samu a lokacin marigayi Nasser. An shirya fim ɗin a cikin 1971, kuma bai yi nasara ba a fannin kuɗi, saboda ana yawan dakatar da shi a Gabas ta Tsakiya da ma a Yamma (yafi Turai). Sai dai ya sami yabo bayan shekaru talatin da biyar. Har yanzu an haramta shirin a ƙasashe da dama, musamman a ƙasashen Larabawa.
Kamfanin Founoon ne ke rarraba fim ɗin kuma an fassara shi cikin Faransanci da Ingilishi.