Colin Udoh

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Colin Udoh
Rayuwa
Haihuwa Port Harcourt, 20 century
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan jarida

Colin Udoh ɗan jaridar Najeriya ne kuma mai gabatar da shirye-shiryen talabijin na wasanni.

A halin yanzu Colin yana aiki da Kwese Sports.

Ya kasance mai sharhi a matsayin mai nazari na gidan talabijin na Super Sport kuma ya rubuta wa mujallar kwallon kafa ta Afirka Kick Off. Yayi aiki da hukumar kwallon kafa ta Najeriya a matsayin jami’in yaɗa labarai.

Udoh ya auri 'yar wasan kwallon kafa ta Najeriya Mercy Akide.[1]

A wata hira da ya yi da manema labarai, ya bayyana yadda aiki a matsayin jami’in yaɗa labaran Najeriya ya kasance abin jin dadi, amma ta wani ɓangaren abin takaici. Duk da bacin rai, ya ce ba zai canza kwarewa da komai ba.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Enyadike, Emeka (18 January 2011). "Q & A with Mercy Akide-Udoh". Super Sport. Retrieved 30 March 2012.
  2. Macintosh, Iain. "Vox in the Box: Colin Udoh". The Set Pieces. Retrieved 11 November 2022.