Cornelis August Wilhelm Hirschman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cornelis August Wilhelm Hirschman
Dictator of fifa (en) Fassara

1918 - 1920
Daniel Burley Woolfall - Jules Rimet (en) Fassara
Secretary General of FIFA (en) Fassara

1906 - 1931
Louis Muhlinghaus (en) Fassara - Ivo Schricker (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Medan, 16 ga Faburairu, 1877
ƙasa Kingdom of the Netherlands (en) Fassara
Mutuwa Amsterdam, 26 ga Yuni, 1951
Sana'a
Sana'a Ma'aikacin banki da ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Cornelis August Wilhelm Hirschman[1] (Sha shida Fabrairu 1877 - ashirin da shida ga Yuni 1951), wanda aka fi sani da Carl Anton Wilhelm Hirschman,[2] ma'aikacin banki ne na Holland, wanda ya kafa FIFA a shekara ta 1904 kuma Babban Sakatare na FIFA na biyu, yana aiki daga shekara ta 1906 zuwa 1931.[3] A shekarar 1912 kuma ya kasance daya daga cikin wadanda suka kafa kwamitin Olympics na kasar Holland (NOC). [4]

Lokacin da shugaban FIFA Daniel Burley Woolfall ya mutu a shekara ta 1918, Hirschman ya kiyaye kungiyar daga rugujewa, kusan shi kadai kuma a kan kansa, yana aiki daga ofisoshinsa a Amsterdam. Shi ne shugaban riko na FIFA har sai da Jules Rimet ya zama shugabanta na uku a watan Maris shekara ta 1921.

Bayan Crash na shekarar 1929 Kamfanin kasuwancin hannun jari na Hirschman ya yi fatara kuma kudaden da ya saka wa NOC da FIFA sun yi hasara. Hirschman ya yi murabus ba zato ba tsammani daga NOC da FIFA a shekarar 1931.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]