Cynthia Mamle Morrison

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cynthia Mamle Morrison
Member of the 8th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2021 -
Election: 2020 Ghanaian general election (en) Fassara
Minister for Gender, Children and Social Protection (en) Fassara

8 ga Augusta, 2018 - 6 ga Janairu, 2021
Member of the 7th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2017 -
District: Agona West Constituency (en) Fassara
Election: 2016 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Elmina, 17 ga Janairu, 1964 (60 shekaru)
ƙasa Ghana
Mazauni Elmina
Karatu
Makaranta unknown value certificate (en) Fassara : unknown value
Accra Girls Senior High School
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, darakta da Malami
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa New Patriotic Party

Cynthia Mamle Morrison (an haife ta 17 Janairu 1964) 'yar siyasa ce 'yar Ghana kuma memba ce a Sabuwar Jam'iyyar Patriotic. A halin yanzu ita ce ‘yar majalisa mai wakiltar mazabar Agona ta Yamma. A ranar 9 ga watan Agusta 2018, Shugaba Nana Akufo-Addo ya nada ta Minista mai kula da jinsi, yara da kare zamantakewa.[1][2][3] Ta kasance ministar jinsi, yara da kare zamantakewa.[4][5]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Cynthia Morrison a ranar 17 ga Janairun 1964 a Elmina a yankin Tsakiya.[6] Ta sami Takaddar Horar da Malamai a Makarantar Koyarwa ta Maria Montessori a 1992 da kuma a Hepziba Montessori.[7] Haka nan tana da takaddun shaida a cikin abinci daga Flair Catering.[8]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ita ce babbar Darakta kuma Manaja ta kamfaninta.[8] Ta kuma kasance Mai mallakar Maryland Montessori a Dansoman.[6] A halin yanzu ita ce ministar jinsi, yara da kare zamantakewa ta kasar Ghana.[9][10][11]

Tallafawa[gyara sashe | gyara masomin]

Cynthia Morrison ta ba da gudummawar kayayyaki da suka haɗa da kujerun ƙafafu, masu horar da makafi da masu kula da sanduna a wani ɓangare na bikin cikarta shekaru 52 da haihuwa.[12]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Morrison ita memba ce a 'New Patriotic Party'. A halin yanzu ita ce ‘yar majalisa mai wakiltar mazabar Agona ta Yamma a yankin tsakiyar kasar.[13][14]

Zaben 2016[gyara sashe | gyara masomin]

Ta lashe wannan kujera a lokacin babban zaben Ghana na 2016. Wasu ‘yan takara biyu da suka hada da Charles Obeng-Inkoom na 'National Democratic Congress' da Evans Idan Coffie of Convention People’s Party su ma sun fafata a zaben 2016 na mazabar Agona ta Yamma da aka gudanar a shekarar 2016.[15][16][17] Cynthia ta lashe zaben ne da samun kuri'u 32,770 daga cikin 56,878 da aka kada, wanda ke wakiltar kashi 58.03 na jimillar kuri'un da aka kada.[6]

Zaben 2020[gyara sashe | gyara masomin]

Ta tsaya takara a babban zaben Ghana na 2020 a matsayin 'yar takarar majalisar dokoki ta. 'New Patriotic Party' kuma an zabe ta a karo na biyu na shekaru hudu.[18] Ta samu kuri'u 30,513 daga cikin jimillar kuri'u 59,193 da aka kada yayinda Paul Ofori-Amoah na jam'iyyar adawa ta 'National Democratic Congress' ya samu kuri'u 27,673,[18] sannan dan takara mai zaman kansa Isma'il Kofi Tekyi Turkson ya samu kuri'u 1,007.[19]

Kwamitoci[gyara sashe | gyara masomin]

Ita ce shugabar kwamitin tabbatar da gwamnati sannan kuma shugabar kwamitin sadarwa.[13]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Ta auri Herbert Morrison tana da ‘ya’ya bakwai.[20] Ta bayyana a matsayin Kirista.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "'I am a submarine politician' - Gender minister-designate eager to make impact" (in Turanci). Archived from the original on 10 August 2018. Retrieved 2018-11-01.
  2. "Agona West NDC congratulates Cynthia Morrison". www.ghanaweb.com (in Turanci). Retrieved 2018-11-01.
  3. "Borstal homes are my priority - Gender Minister-nominee Cynthia Morrison". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2018-11-01.
  4. "National Coordinator of School Feeding Programme sacked - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). Retrieved 2021-05-19.
  5. "Glitz top 100 inspirational women – Page 100 – Glitz Africa Magazine" (in Turanci). Retrieved 2022-05-28.
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 "Morrison, Cynthia Mamle". Ghana MPS (in Turanci). Retrieved 2022-11-20.
  7. "Ghana MPs - MP Details - Morrison, Cynthia Mamle". www.ghanamps.com. Retrieved 2019-03-02.
  8. 8.0 8.1 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2019-03-02.
  9. "CLOTTEY KORLEY CONSTITUENCY BENEFITS FROM THE GOG-FBO's FOOD DONATION TO THE NEEDY : Ministry of Gender, Children and Social Protection". www.mogcsp.gov.gh. Retrieved 2020-07-19.
  10. "ENCOURAGE & SUPPORT ALL CONTESTANTS TO UNDERTAKE PROJECTS – HON. CYNTHIA MORRISON TO MISS GHANA EXECUTIVES : Ministry of Gender, Children and Social Protection". www.mogcsp.gov.gh. Retrieved 2020-07-19.
  11. "Hon. Cynthia Morrison empower Agona West Children through ICT and Entrepreneur Programmes". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2020-07-19.
  12. Arthur, Christopher. "Cynthia Morrison Cerebrates Her 52 Birthday with the People with Disability".
  13. 13.0 13.1 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2022-11-20.
  14. "Parliament approves construction of TVET facility at Agona West - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). 2020-11-18. Retrieved 2022-11-20.
  15. "Ghana Election 2016 Results - Agona West Constituencywebsite=Ghana Elections". Peace FM. Retrieved 2019-03-14.
  16. "NPP Primatries: Cynthia Morrison Retains Agona West Seat". Peacefmonline.com - Ghana news. Retrieved 2020-07-19.
  17. "Don't impose incumbent MP on Agona West - Concerned Delegates". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-07-19.
  18. 18.0 18.1 "Agona West Constituency: Cynthia Morrison re-elected as MP". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2022-11-20.
  19. FM, Peace. "2020 Election - Agona West Constituency Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2022-11-20.
  20. "Cynthia Morrison - Changed lives of Ghana's conjoined twins". Graphic Online (in Turanci). 2014-01-18. Retrieved 2019-03-02.