Dame Virginia Ngozi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dame Virginia Ngozi
Gwamnan jahar Anambra

3 Nuwamba, 2006 - 9 ga Faburairu, 2007
Peter Obi - Peter Obi
Rayuwa
Cikakken suna Virginia Ngozi Etiaba
Haihuwa 11 Nuwamba, 1942 (81 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Tarihin Mutanen Ibo
Harshen uwa Harshen Ibo
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Kyaututtuka

Dame Virginia Ngozi Etiaba, CON. (an haife ta ranar 11 ga watan Nuwamba, 1942). Tsohuwar Gwamniyar Jihar Anambra, dake kudu maso gabashin Nijeriya ce, daga Nuwamba shekarar 2006 zuwa Fabrairu 2007. hakan yasa ta zama mace ta farko a tarihin Najeriya da ta zama gwamna. An sanya ta ne yayin da majalisar dokokin jihar ta tsige gwamnan da ya gabata, Peter Obi saboda zargin rashin ɗa'a. Ta mayar da ikonta ga Obi watanni uku bayan haka lokacin da kotun daukaka kara ta soke tsigewar.[1]

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

Etiaba yar asalin Ezekwuabor Otolo-Nnewi ne a karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra. Kawun ta Cif Pius Ejimbe ne ya daga ta daga makarantar sakandare a Kano Nijeriya har sai da ta auri Marigayi Bennet Etiaba na Umudim Nnewi.[2]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kwashe shekaru 35 tana aiki a matsayin malami sannan ta shugabanci makarantu da dama a Kafanchan, Aba, Port Harcourt, da Nnewi . Ta yi ritaya daga aikin Gwamnatin Jihar Anambra a 1991 kuma ta kafa Makarantun Tunawa da Bennet Etiaba, Nnewi, wanda ta kasance mallakin ta. A watan Maris na 2006 ta yi murabus domin karbar mukamin Mataimakin Gwamnan Jihar Anambra.

Etiaba ta kasance mamba a kungiyar mata ‘yan kasuwa, Shirin Ilimi na kasa da kasa na karamar hukumar Nnewi ta Arewa, da Environmental International Vanguard da kungiyar kula da ilimin yara ta duniya (OMEP). Ta kuma kasance membobin kungiyar Synod na Cocin na Najeriya (Anglican Communion), memba a kungiyar Kiristocin Makarantun Najeriya, memba a kwamitin gwamnoni na Makarantar Grammar Memorial ta Okongwu ta Nnewi, memba a kwamitin gwamnonin yara masu tsarki. Makarantar Convent, Amichi da kuma essoran sanda mai kula da Kotun Matasa na gundumar Nnewi.

Etiaba ita ce mahaifiyar yara shida wanda ɗayansu shine Emeka Etiaba (SAN), wanda ya taɓa tsayawa takarar kujerar gwamna a jihar Anambra.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]