Dambu
Dambu | |
---|---|
Kayan haɗi | Masara |
Kayan haɗi | Zogale, cooking oil (en) , gishiri, albasa da Couscous |
Tarihi | |
Asali | Nijar da Najeriya |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Dambu, wani kalan abinci ne wanda ya samo asali a kasar Hausawa a tarihi. Dambu abinci ne da ba kowace mace ta iya yinshi ba, hasali ma koda mace ta kware wajen yin danbu, to fa wata rana sai ya bada ita (sai ya kiyi, wato yayi mata gardama a wani bangare) ya kan iya shake mutum Musamman idan ana cin shi babu ruwa a kusa.
Dambu yana da farin jini a wurin dattijai har ma da samari idan su kayi marmarin shi.
Yakan haifar da koshi  dan danan idan aka sanya mishi hadin kuli-kuli.
Dambu Abincin hausawa ne da'ake yin shi da Tsakin masara ko shinkafa da Rama ko Yakuwa ko zogale ko kabeji. Ana dafawa ne ta hanyar yin Siraci.
Rabe-raben dambu
Shi dai dambu yakasu kashi kashi akwai dambun tsakin masara akwai kuma na dambun shinkafa amma wanda. Yafi tasiri a gargajiyan ce shine dambun tsakin masara wanda mafi yawan mutanen najeriya suna cinshi musamman dan arewa.[1][2]
Dambu yana da nau'i biyu
[gyara sashe | gyara masomin]Dambun tsakin masara
Dambun barjajjiyar shinkafa.
Dambun barjajjiyar alkama
Har dambun garin masara anayi yanzu. Wasu mutane su kan ci shi da mai da yaji, wasu su ci shi da miyan dage-dage.
Kayan yin dambu
[gyara sashe | gyara masomin]A nayin Dambu da tsaki (barjin inji wanda yake da laushi amma ba sosai ba) ko na masara, ko dawa, gero,har ma dana shinkafa.
Yadda ake yin dambu
[gyara sashe | gyara masomin]Dambu idan ka samu tsaki wanda aka ɓarza, da tafasa ko ganyen zogale,ko Ganye Alaiyaho,ko kuma wani nau'in ganye da muke amfani da shi, ka samu ruwa, gishiri Maggi.sai ka dora tukunya karfe a wuta ko ainahin tukunyar yin dambon sai kasaka ruwan bamasu yawa ba daga Nan sai ka kawo tukunya ta kasa wadda a kasanta fasasshe ne sai a dora ta a wannan tunkunya karfe da aka sa ruwa sai a kwaba wani abun dorawa, ko kuma duk wani abunda za'a iya amfani dashi don like tunkunya biyu. Bayan ka like su sai ka samu wani dan murfi wanda zai shiga cikin bakin tukunya kasa dinnan tunda daman nache za'a fasa kasan tunkunya, sai kasa wannan murfin yadda dai ruwan nan idan ya tafasa suracin shi zai dinga tasowa cikin tukunya kasa dinnan. Bayan kasa murfin sai ka zuba tsaki ka/ki da ka gyara shi ka/ki jika ba sosai ba kasa gishiri Maggi ganye zogale ko tafasa, sai ka sake rufewa. Bayan yayi idan ka sauke daman ka tanada man gyada soyayye sai a zuba shi roba ayi ta sakuma, kar a manta da ruwan sha ya kasance yana kusa, saboda yana shake makwogwaro.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://cookpad.com/ng/recipes/6141929-dambun-tsakin-masara
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html