David Ombugadu
David Ombugadu | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Suna | Emmanuel |
Shekarun haihuwa | 1978 |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | mamba a majalisar wakilai ta Najeriya, |
Ilimi a | Jami'ar, Jos da Jami'ar jihar Riba s |
David Emmanuel Ombugadu ɗan siyasar Najeriya ne wanda ya kasance ɗan majalisar wakilai a Najeriya mai wakiltar Akwanga, Wamba da Nassarawa Eggon daga shekarar 2011 zuwa 2019. Ya tsaya takarar gwamnan jihar Nasarawa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2019.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Emmanuel Ombugadu a ranar 10 ga watan Janairun shekarar 1978. Ya halarci makarantar firamare ta LEA Kakuri a jihar Kaduna.[1][2] A cikin shekara ta 1995, ya halarci Kwalejin Gwamnati da ke Keffi inda ya samu takardar shaidar SSCE. Daga nan ya wuce Jami’ar Jos don samun digiri na farko (Bsc) a fannin tattalin arziƙi a cikin shekarar ta 2001.[3]
Daga baya ya ci gaba da yin NYSC a cikin shekarar ta 2003. Ya ci gaba da yin digirinsa na biyu (Msc.) a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas.[4]
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Emmanuel Ombugadu ya kasance memba na kwamiti a cikin kwamitin masu zaman kansu da kasuwanci,[5] dokoki da kwamitin kasuwanci[6] da kwamitin asusun jama'a har zuwa watan Mayun shekara ta 2015.[7][8]
Daga nan ya ci gaba da tafiyar da harkokinsa na siyasa inda ya tsaya takarar majalisar wakilai ta Nasarrawa[9]daga shekara ta 2011 zuwa 2015[10] da kuma shekara ta 2015 zuwa 2019.[11]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jerin sunayen 'yan majalisar wakilan Najeriya a shekara ta 2015 zuwa 2019
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Teachers' strike: NUT taskforce locks Kaduna schools". newtelegraphonline.com (in Turanci). Retrieved 2018-06-25.[permanent dead link]
- ↑ "About Davematics". www.ombugadu.com (in Turanci). Archived from the original on 2018-08-10. Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "Biography of Emmanuel David Ombugadu". www.nigerianbiography.com. Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "NGP KYG: Hon. Davematics Ombugadu Emmanuel David". kyg.nigeriagovernance.org. Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "Government Policy on Privatization And Commercialization on Nigeria Economy - ArticlesNG". ArticlesNG (in Turanci). 2017-01-03. Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "Senate Committee on Rules and Business Archives - INFORMATION NIGERIA". INFORMATION NIGERIA (in Turanci). Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "Senate Committee on Rules and Business Archives - INFORMATION NIGERIA". INFORMATION NIGERIA (in Turanci). Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "Emmanuel Ombugadu :: Shine your eye". www.shineyoureye.org. Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "LIST - New House of Reps Members for Nigeria's 8th National Assembly - Premium Times Nigeria". Premium Times Nigeria (in Turanci). 2015-05-02. Retrieved 2018-06-25.
- ↑ "List Of House of Representatives Members - 2011-2015". www.nigerianelitesforum.com (in Turanci). Archived from the original on 2016-09-01. Retrieved 2018-06-25.
- ↑ Yakubu, Dogara (9 June 2015). "HOUSE OF REPRESENTATIVES FEDERAL REPUBLIC: OF NIGERIA VOTIES AND PROCEEDINGS". National Assembly Press. Retrieved 9 June 2015.