Edema Fuludu
Appearance
| mutum | |
| Bayanai | |
| Jinsi | namiji |
| Shekarun haihuwa | 8 Mayu 1970 |
| Wurin haihuwa | Burutu |
| Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa |
| Matsayin daya buga/kware a ƙungiya | Mai buga tsakiya |
| Mamba na ƙungiyar wasanni | Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya |
| Wasa | ƙwallon ƙafa |
Edema Godmin Fuludu (an haife shi a ranar 8 ga watan Mayun 1970) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya. Ya buga ƙwallo a kulob ɗin New Nigerian Bank da BCC Lions da Julius Berger da ke Najeriya da Altay a Turkiyya, sannan ya buga wa tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya wasa a ƙasashen duniya.[1] Ya kasance cikin tawagar ƴan wasan Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1994.[2] Fuludu ya yi aiki a matsayin kocin Warri Wolves.[3]