Jump to content

Eliad Moreh

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Eliad Moreh
Rayuwa
Haihuwa Faris
ƙasa Faransa
Isra'ila
Karatu
Harsuna Faransanci
Ibrananci
Turanci
Sana'a
Sana'a curator (en) Fassara

Eliad Moreh (an haife ta a birnin Paris na ƙasar Faransa ) Yar ƙasar Isra'ila ne, wanda take daya daga cikin mutanen da suka tsira a munanan hare-haren ta'addanci a Jami'ar Ibraniyawa da ke Urushalima a ranar 31 ga Yuli, 2002.

Bayan tashin bama-bamai, an rarraba hotunan Eliad a ko'ina cikin duniya, kuma an yi hira da ita a cikin New York Post, Fox News a tsakanin sauran labaran duniya.

Tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2005, Eliad ta halarci tawaga da dama na wadanda ta'addanci ya shafa, ta kuma gana da manyan jami'ai a Turai da Amurka A matsayinta na wanda ta tsira daga ta'addancin masu tsattsauran ra'ayin Islama, Moreh ta yi imani da cewa masu sa ido a yammacin duniya dole ne su yi Allah wadai da ta'addanci kowane iri kuma su dauki tsattsauran ra'ayi.[1] Masu kishin Islama suna barazana ga kasashen yammacin duniya da al'adu marasa rinjaye.

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Eliad a birnin Paris kuma ta koma Isra'ila tana da shekaru 18. Ta sami BA a Tarihin Fasaha da Adabin Turanci sannan ta sami MA a Tarihin Fasaha daga Jami'ar Hebrew a Urushalima. A 2002 ta yi aiki a matsayin mai bincike a Cibiyar Nazarin Yahudanci a wannan jami'a. [2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]