Jump to content

Eno James Ibanga

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Eno James Ibanga
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da physicist (en) Fassara

Eno James Ibanga About this soundsaurara, masanin ilimin Najeriya ne. Shi farfesa ne a fannin kimiyyar lissafi/materials science. Yana aiki a matsayin mataimakin shugaban Jami'ar Jihar Akwa Ibom (AKSU). A ranar 3 ga watan Agusta 2020, Mai Girma Gwamna Udom Gabriel Emmanuel ya naɗa Farfesa Eno James Ibanga a matsayin kwamishina a ma'aikatar ayyuka da kashe gobara. Yana da aure da ƴaƴa.

James Ibanga ya samu digirin digirgir a fannin kimiyyar lissafi ta Solid State a shekarar 2000 a jami'ar Najeriya dake Nsukka.

Ibanga ya fara aikinsa a matsayin malamin jami'a a jami'ar Calabar a shekarar 1982. An naɗa shi Farfesa a fannin Physics a Jami’ar Uyo a shekarar 2008 da kuma Shugaban Sashen fannin, Physics da Shugaban Harkokin Ɗalibai. Ibanga malamin Physics ne. Ya kasance Mataimakin Farfesa a Jami'ar Jihar Nassarawa, Keffi, a 2004, kuma Babban Malami, Jami'ar Aikin Noma, Makurdi a 2002. Ya yi koyarwa a Jami’ar Aikin Gona ta Abeokuta a shekarar 1986.

Ibanga ya kasance malami mai ziyara a cibiyoyi daban-daban ciki har da Jami'ar Jihar Akwa Ibom daga 2009 - 2013, Jami'ar Jihar Benue, Makurɗi, 2006-2011 da Jami'ar Agriculture, Makurdi, 2007-2010. Ma'aikacin jarrabawar waje ne a Jami'ar Abuja; Ladoke Akintola University of Science and Technology, Ogbomosho; Jami'ar Ilorin da Jami'ar Obafemi Awolowo. Ya kasance memba a Majalisar Dattawa, Boards da kwamitoci a waɗannan Jami'o'in. Ya yi hidima a NUCa matsayin memba, sannan kuma shugaban kwamitin tantance shirye-shiryen digiri a fannin (Physical Sciences).

  • "Akwa Ibom State University". www.aksu.edu.ng (in Turanci). Archived from the original on 11 April 2018. Retrieved 11 April 2018.