Eugène Rutagarama

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Eugène Rutagarama
Rayuwa
ƙasa Ruwanda
Sana'a
Sana'a environmentalist (en) Fassara
Kyaututtuka
hoton Eugene
hoton eugene

Eugène Rutagarama, masanin muhalli ne daga Ruwanda . An ba shi lambar yabo ta " Goldman Environmental Prize " a shekara ta 2001, saboda ƙoƙarin da ya yi na ceton al'ummar gorilla na dutse a cikin gandun dajin Volcanoes a tsaunin Virungas, a lokacin yaƙi da tashe-tashen hankula na baya-bayan nan a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo .[1]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Tun daga shekarar 2001, Rutagarama ya ci gaba da yin ayyukan kiyayewa, yana ba da gudummawa ga sauƙaƙe ayyukan haɗin gwuiwar duniya da nufin kare Central Albertine Rift, yankin da aka sani da flora da fauna daban-daban, ciki har da mazauni na yanayin gorillas na dutsen Virunga. Eugène ya kuma riƙe manyan muƙamai a ƙungiyar kare namun daji, Cibiyar Bincike ta Karisoke ta Dian Fossey Gorilla Fund, da kuma hukumar kula da wuraren shakatawa na ƙasar Rwanda, bayan yakin 1994 da kisan ƙare dangi. A halin yanzu, Eugène yana aiki a matsayin babban mai ba da shawara kan kiyayewa a Wild Earth Allies, inda ya mai da hankali kan kiyaye wuraren zama na gorilla ta hanyar haɓaka ci gaban al'umma. [2] Shekaru biyu bayan an ba shi lambar yabo ta Goldman, Rutagarama ya ɗauki matsayin darektan Shirin Kare Gorilla na Duniya (IGCP). Ya yi aiki a wannan aikin na tsawon shekaru tara. A cikin shekarar 2012, an naɗa Rutagarama a matsayin babban mai ba da shawara na fasaha ga Greater Virunga Transboundary Collaboration, ƙungiyar gwamnatocin da DR Congo, Rwanda, da Uganda suka kafa tare da taimakon IGCP.[3][4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Goldman Environmental Prize: Eugène Rutagarama Archived 2007-10-30 at the Wayback Machine (Retrieved on November 10, 2007)
  2. "Eugène Rutagarama - Goldman Environmental Prize" (in Turanci). 2022-03-18. Retrieved 2023-04-19.
  3. "Throwback Thursday: 2001 Goldman Prize Winner Eugene Rutagarama - Goldman Environmental Prize" (in Turanci). 2014-03-20. Retrieved 2023-04-19.
  4. "IGCP coalition celebrates 20th anniversary and launches effort to develop new strategy". African Wildlife Foundation (in Turanci). Retrieved 2023-04-19.