Jump to content

Eugenia Date-Bah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Eugenia Date-Bah
Rayuwa
ƙasa Ghana
Ƴan uwa
Abokiyar zama Samuel Date-Bah
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Malami da marubuci
Kyaututtuka
Mamba University of Ghana

Eugenia Date-Bah kwararriya ce a fannin ilimi 'yar ƙasar Ghana ce kuma marubuciya. Ta kasance memba a sashin ilimin zamantakewa na Jami'ar Ghana.[1] An zaɓe ta a matsayin fellow a Kwalejin fasaha da Kimiyya ta Ghana a shekara ta 2005.[2] Date-Bah ta taɓa zama Daraktar InFocus, shirin kungiyar Kwadago ta ƙasa da ƙasa da ke mai da hankali kan magance rikice-rikice da sake ginawa, ta taɓa zama manajar shirin ayyukan kungiyar kwadago ta ƙasa da ƙasa don samar wa ƙasashen da suka fito daga faɗace-faɗacen makamai da kwarewa da horar da 'yan kasuwa.[3]

Date-Bah ita ce matar malamin fikihu mai ritaya; Samuel Kofi Date-Bah.[4]

  • Female and Male Factory Workers in Accra (in Christine Oppong's Female and Male in West Africa), (1982);
  • Sustainable Peace After War: Arguing the Need for Major Development in Conflict programming, (1996);
  • Jobs After War: A Critical Challenge in the Peace and Reconstruction Puzzle, (2003);;
  • Lest We Forget: Insights Into the Kenya's Post Election Violence (with Rita Njau, Rosabelle Boswell), (2008).
  1. Ghana Journal of Sociology (in Turanci). Ghana Sociological Association. 1976.
  2. Sciences, Ghana Academy of Arts and (2006). National Integration (in Turanci). Ghana Academy of Arts and Sciences. ISBN 978-9964-950-27-9.
  3. Manji, Firoze; Burnett, Patrick (2005). African Voices on Development and Social Justice: Editorials from Pambazuka News 2004 (in Turanci). Fahamu/Pambazuka. ISBN 978-9987-417-35-3.
  4. "Chairman of University Council Authors Book on the Supreme Court of Ghana | University of Ghana". www.ug.edu.gh. Archived from the original on 2023-11-08. Retrieved 2021-03-09.