Jump to content

Ezira

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ezira
Bayanai
Ƙasa Najeriya
ezira
ezira

Ezira Gari ne na Igbo a kudu maso gabashin Najeriya karamar hukumar Orumba ta Kudu, jihar Anambra, Ezira kuma ana kiranta da Eziha (Ozi Mba Ihe) wanda ke nufin " nuna wa wasu haske" a cikin yaren 'yan asalin. Yana da kauyuka hudu sune Obuotu, Ubaha, Imoohia da Okii, wanda Obuotu shine babban kauyukan.

Ezira tsohon gari ne da aka sani da duban rana, kuma yana kewaye ne da Umunze, Isulo, Eziagu, Umuchu da Achina. Ana kyautata zaton Ezira shine Gari mafi dadewa a yankin, tare da tatsuniyoyi da suka samo asali tun karni na tara miladiyya, kamar yadda binciken ilimin kimiyyar tarihi na ayyukan fasaha na ƙarfe, tagulla, ƙararrawa, mundaye da tukwane a Ezira ya bayyana.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.