Faith Tabernacle
Faith Tabernacle | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | jahar Legas |
Birni | Lagos, |
Coordinates | 6°41′N 3°10′E / 6.68°N 3.17°E |
Offical website | |
|
Faith Tabernacle megachurch ne na bishara kuma hedkwatar cocin Living Faith Church Worldwide. Tana a Canaanland, Ota, Lagos, Nigeria, halin yanzu neo-charismatic movement. Babban Fasto na wannan al’umma shine Dokta David Oyedepo tun kafuwarta a 1983. A cikin shekarar 2015, mutane 50,000 ne suka halarta.
Fage
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar 1981, David Oyedepo yana da shekaru 26, yana da hangen nesa game da hidimarsa. [1] An kafa Cocin a ranar 11 ga watan Disamba, 1983. [2] A cikin shekarar 2014, Living Faith Church Worldwide tana cikin ƙasashe 65. A cikin shekarar 2020, Tabernacle na Faith tana da halartan mutane 50,000.
Gine-gine
[gyara sashe | gyara masomin]An sanyo ƙasar Kan'ana a cikin shekarar 1998 kuma an fara 560 acres (2.3 km2) , tana cikin Ota, Ogun, Nigeria. An gina hedkwatar cocin na duniya, Tabernacle, a Cannanland tsakanin 1998 zuwa 1999, tana ɗaukar watanni goma sha biyu ana kammalawa. An kafa harsashin ginin a ranar 29 ga watan Agusta, 1998.
A cikin shekarar 1999, an buɗe wurin Faith Tabernacle da kujeru 50,400. An yi la'akarin Faith Tabernacle ta zama coci mafi girma a duniya dangane da iya aiki. [3] [4] [5] Tana da faɗin ƙasa hekta 70 kuma an gina ta a cikin rukunin da ake kira Canaanland, wanda girmanta ya haura hekta 10,500 (kilomita 42) a Ota, wani yanki na Legas. An gina ginin cocin a ƙarƙashin watanni 12 kuma an keɓe shi a cikin watan Satumba 1999. [6]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]
- Jerin manyan wuraren taro na cocin bishara
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Pieter Coertzen, M Christiaan Green, Len Hansen, Law and Religion in Africa: The quest for the common good in pluralistic societies, African Sun Media, South Africa, 2015, page 310
- ↑ Martin Lindhardt, Pentecostalism in Africa: Presence and Impact of Pneumatic Christianity in Postcolonial Societies, BRILL, Netherlands, 2014, page 115
- ↑ Candy Gunther Brown, Global Pentecostal and Charismatic Healing, Oxford University Press, UK, 2011, page 253
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedBBC
- ↑ Israel O. Olofinjana, 20 Pentecostal Pioneers in Nigeria: Their Lives, Their Legacies, Xlibris Corporation, USA, 2011, page 127
- ↑ Vinson Synan, J. Kwabena Asamoah-Gyadu, Amos Yong, Global Renewal Christianity: Spirit-Empowered Movements: Past, Present and Future, Charisma Media, USA, 2016, page 28
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- faithtabernacle.org.ng Official Site