Fasa gidan yari a Kogi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentFasa gidan yari a Kogi
Iri aukuwa
Bangare na prison escape (en) Fassara
Kwanan watan 2 Nuwamba, 2014
Wuri Jihar Kogi
Adadin waɗanda suka rasu 1
Adadin waɗanda suka samu raunuka 0

Fasa gidan yarin na Kogi wani hari ne da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba da ake kyautata zaton ƴan kungiyar ta’adda ta Boko Haram ne, sun kai hari a gidan yarin Koto-Karffi da ke jihar Kogi a arewa maso tsakiyar Najeriya.[1] Harin ya faru ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2014.[2] Kimanin fursunoni 144 ne suka tsere daga gidan yarin; An harbe fursuna 1 tare da kashe shi yayin harin.[3] Fursunonin da suka tsere sun kasance suna jiran shari'a ne bisa laifin fashi da makami.[4] Fursunonin 12 sun koma gidan yarin don cika hukuncin da aka yanke musu[5] kuma kusan fursunoni 45 da suka tsere an sake kamo su baki ɗaya.[6][7]

Lamarin[gyara sashe | gyara masomin]

An ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 2 ga Nuwamba, 2014.[8] Harin dai yana da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram, kungiyar masu tada ƙayar baya a arewa maso gabashin Najeriya.[9] Alhaji Aminu Sule, babban kwanturolan hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya, ya yi iƙirarin cewa aikin fasa gidan yarin ya samu nasara ne sakamakon rashin samun kudaden gudanar da ayyukan gidan yari[10] kuma ba a canza salon gidan yarin ba tun lokacin da aka kafa gidan yarin a shekara ta 1934.[11]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "BBC News - Nigeria jailbreak: Boko Haram claims Kogi prison attack". BBC News. 16 February 2012. Retrieved 24 December 2014.
  2. "Boko Haram invades Kogi prison, frees 143". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 9 December 2014. Retrieved 24 December 2014.
  3. "Jailbreak in Kogi; gunmen free 144 inmates - Premium Times Nigeria". Premium Times Nigeria. 3 November 2014. Retrieved 24 December 2014.
  4. "KOGI JAILBREAK UPDATE: 12 escaped inmates re-arrested – Prison service". TODAY. Archived from the original on 24 December 2014. Retrieved 24 December 2014.
  5. "Kogi jail break: 12 inmates re-arrested". DailyPost Nigeria. 3 November 2014. Retrieved 24 December 2014.
  6. Gbenga Omokhunu, Abuja. "Kogi jail break: 45 fleeing inmates recaptured". The Nation. Retrieved 24 December 2014.
  7. "Police Rearrests Kogi Prison Break Escapee". Channels Television. Retrieved 24 December 2014.
  8. daniel (4 November 2014). "Kogi Jail Break: 12 Escaped Inmates Re-Arrested". INFORMATION NIGERIA. Retrieved 24 December 2014.
  9. "Kogi jailbreak: Moro gives ultimatum to contractor". Vanguard News. 6 November 2014. Retrieved 24 December 2014.
  10. Cyril Mbah, Abuja. "Kogi jailbreak: Need for improved justice, prison system". Newswatch Times. Archived from the original on 24 December 2014. Retrieved 24 December 2014.
  11. "Kogi Jail Break: Gunmen Attack Prison, Free 145 Inmates - Nigerian News from Leadership Newspapers". Nigerian News from Leadership Newspapers. Retrieved 24 December 2014.