Fatima al-Batayahiyyah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fatima al-Batayahiyyah
Rayuwa
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Fāțima bint Ibrahim ibn Mahmud al-Bațā'ihiyya wacce aka fi sani da Fatima al-Batayahiyyah ta kasance musulma malamar hadisi a ƙarni na 8.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Fatima al-Batayahiyyah ta koyar da Sahihul Bukhari a Damascus . An san ta a matsayin daya daga cikin manya-manyan malamai na wancan lokacin, ta nuna musamman a lokacin aikin Hajji lokacin da manyan malamai mazan zamanin suka yi ta tururuwa daga nesa don jin magana daga bakin ta Kai tsaye.

Da ta tsufa sai ta koma Madina ta koyar da dalibanta na kwanaki a masallacin Annabi da kansa. A duk lokacin da ta gaji, ta kan kwantar da kanta a kan kabarin Muhammad (S.A.W), ta ci gaba da koyar da dalibanta. Wannan al'adar ta bambanta da abin da ake yi a yau, inda ba a yarda mutane su kalli wurin hutun Muhammadu ba.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]