Felicia Adeyoyin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Felicia Adeyoyin
Rayuwa
Haihuwa 6 Nuwamba, 1938
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1 Mayu 2021
Karatu
Makaranta Abeokuta Grammar School
Sana'a
Sana'a university teacher (en) Fassara

Felicia Adebola Adeyoyin (6 Nuwamba 1938 - 1 Mayu 2021) farfesa ce a Jami'ar Legas kuma gimbiya daga gidan mai mulki na Iji na Saki, Jihar Oyo. Ita ce mawallafiyar waƙar alƙawarin ƙasa na Nijeriya .[1]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Felicia Awujoola a ranar 6 ga Nuwamba 1938 a Ogbomoso, Jihar Oyo.[2][3] Ta halarci Makarantar Baptist Baptist ta Idi-Aba daga 1953 kuma ta kammala a 1957 a fannin (teacher programme). [2] A 1965 ta auri Solomon Adedeji Adeyoyin, wanda ya halarci makarantar kanin Idi-Aba's brother school. [3][2]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Ta sami digiri na farko tare da girmamawa a fannin (Geography) daga jami'ar Birkbeck, University of London a 1968 har wayau ta sami Diploma na Ilimi a jami'ar dai a 1976,[4] sannan ta sami M.A. a Ilimin zamantakewa daga Jami'ar Columbia, New York a 1977, kafin Daga karshe ta samu digirin digirgir a shekarar 1981 a Jami’ar Legas.[5][6]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Adeyoyin Farfesa ce a fannin ilimi a Jami'ar Legas kuma mashawarciyar Majalisar Dinkin Duniya.[2]

A cikin 1976, ta rubuta alkawarin da aka buga 15 ga watan Yuli a jaridar Daily Times a wata kasida mai suna "Loyalty to the Nation, Pledge". Shugaban kasa na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya gyara alkawarin tare da gabatar da shi a matsayin waƙar alkawari ta ƙasa, inda ya ba da umarnin cewa yara ‘yan makaranta su karanta ta yayin taron asembili (assembly).[7][8][9]

Adeyoyin ta kasance Deaconess of Yaba Baptist Church, Yaba.[2]

Kyauta[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2005, an baiwa Adeyoyin lambar yabo ta kasa, wato Officer of the Order of the Niger (OON).[5]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Adeyoyin ta mutu ne ranar 1 ga watan Mayu 2021 bayan gajeriyar rashin lafiya.[10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Nigeria @ 59: Interesting facts about Nigeria's National anthem, Pledge". The Nation (in Turanci). 2019-10-01. Retrieved 2021-05-06.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 Lawoyin, Oyeronke Alake (2007). IDI-ABA (in Turanci). Xulon Press. ISBN 978-1-60477-072-8.
  3. 3.0 3.1 Who's who in Nigeria (in Turanci). Newswatch. 1990. ISBN 978-978-2704-12-2.
  4. "Notable Birkbeckians: Graduates In Academia". bbk.ac.uk. Birkbeck, University of London. 2021. Retrieved 2021-05-10.
  5. 5.0 5.1 "Author Of Nigeria's National Pledge, Felicia Adedoyin, Is Dead". Gistmaster (in Turanci). 2021-05-05. Archived from the original on 2021-05-05. Retrieved 2021-05-06.
  6. Adeyoyin, Felicia (1977). "The Dynamics of Teaching Social Studies at the Grade Two Teachers' College Level in Lagos State" (PDF).[permanent dead link]
  7. "Author of Nigeria's National Pledge, Felicia Adebola Adedoyin, is Dead". National Mirror. Archived from the original on May 10, 2021. Retrieved 2021-05-10.CS1 maint: unfit url (link)
  8. Joshua, Temi (2021-05-05). "Author of Nigeria's National Pledge, Prof. Felicia Adedoyin, dies at 83". The Daily Page (in Turanci). Retrieved 2021-05-10.
  9. Mbamalu, Socrates (3 May 2021). "Prof. Felicia Adeyoyin, Author of Nigeria's National Pledge, Dies at 83". Foundation For Investigative Journalism.
  10. Akinselure, Wale (2021-05-09). "Saki Indigenes Ask FG, Oyo Govt To Immortalise Late National Pledge Composer". Nigerian Tribune.