Filin jirgin saman Bayelsa na ƙasa da ƙasa
Filin jirgin saman Bayelsa na ƙasa da ƙasa | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jiha | Bayelsa |
Coordinates | 4°17′53″N 6°16′35″E / 4.298°N 6.2764°E |
Altitude (en) | 63 ft, above sea level |
History and use | |
Opening | 14 ga Faburairu, 2019 |
Ƙaddamarwa | 10 ga Faburairu, 2020 |
City served | Yenagoa |
|
Filin jirgin saman Bayelsa (wanda aka fi sani da Bayelsa Cargo Airport ) filin jirgin sama ne na duniya wanda ke Tsibirin Wilberforce, Amassama, Yenogoa, Jihar Bayelsa. Tsohon gwamnan jihar Bayelsa Henry Seriake Dickson ne ya dauki nauyin gina filin jirgin a shekarar 2012.[ana buƙatar hujja] Filin jirgin saman ya fara aiki ne a ranar 14 ga Fabrairu 2019.
Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa Henry Seriake Dickson ne ya kaddamar da tashar jirgin bisa aiki a ranar Litinin, 10 ga Fabrairu 2020 shekara guda bayan tashin ta.
Filin jirgin saman na Bayelsa ya kasance a ranar sha bakwai (17) ga Afrilu 2021 wanda aka ba da izinin ayyukan jirgin kasuwanci daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).