Jump to content

Francis Adenigba Fadahunsi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Fadahunsi Francis Adenigba (an haife shi a ranar 12 ga Yuli 1952) ma'aikacin kwastam ne mai ritaya kuma dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar mazabar Osun ta gabas a majalisar dattawa ta kasa. An haife shi a Ilase-Ijesa a cikin Jihar Osun a ranar 12 ga Yuli 1952 ga marigayi Chief Israel Adekunbi Fadahunsi da Chief (Mrs.) Emily Fadahunsi, dukkansu 'yan asalin Ilase-Ijesa. Fadahunsi ya yi karatun firamare a makarantar firamare ta Anglican ta Saint Paul, Ilase-Ijesa sannan ya yi karatun sakandire a makarantar zamani ta Abebeyin Anglican, karamar hukumar Atakumosa ta yamma a shekarar 1964.[1][2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Chief Fadahunsi of PDP wins Osun East Senatorial seat". www.thenigerianvoice.com. Retrieved 2020-01-24.
  2. "Why I did not support hate speech bill ― Senator Fadahunsi". Vanguard News (in Turanci). 2019-12-29. Retrieved 2022-02-21.