Francisca Oladipo
Francisca Oladipo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Idanre, 15 ga Janairu, 1978 (46 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | Furogirama da computer scientist (en) |
Francisca Onaolapo Oladipo (an haife ta a ranar 15 ga watan Janairu 1978). Farfesa ce 'yar Najeriya a fannin Kimiyyar Kwamfuta, shugaba kuma marubuciya. Tun daga shekarar 2022, ita ce Mataimakiyar Shugaban Jami'ar Thomas Adewumi, Najeriya.[1][2] Kafin naɗin nata, ta kasance Daraktar tabbatar da inganci a Jami'ar Tarayya, Lokoja, Jihar Kogi, Najeriya. Ita ce Babbar Jami'ar Gudanarwa, Virus Outbreak Data Network Africa da Asiya (VODANA).[3][2] Ita ce mace ta farko da ta zama mamba a majalisar gudanarwa a jami'ar tarayya dake Lokoja, sannan kuma mace ta farko shugabar sashin ilimin na'ura mai kwakwalwa a jami'ar.[2][4]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2010, Oladipo ta samu digirin digirgir a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Najeriya.[5] Ta samu Digiri na biyu da Digiri na farko a Jami’a guda. A cikin shekarar 2014, ta kasance abokiyar karatun digiri a Cibiyar Fasaha ta Massachusetts a ƙarƙashin TOTAL-MIT Karfafawa da Ƙaddamar da Malamai.[6][7]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Ta ɓullo da Python Programming Language a cikin Shirin Ilimin Kimiyyar Kwamfuta a Jami'ar Tarayya, Lokoja kuma ta kafa kungiyar PyFUL don haɓaka koyon Programming Language.[8] Ta raba aikinta a PyCon,[9] kuma wasu sun ambaci aikinta akan Python.[10] Oladipo ta kasance mai ba da shawara ga buƙatun buɗaɗɗun bayanai yayin bala'in cutar COVID-19,[11] batun da ta gabatar a cikin wallafe-wallafen[12] da ake bitar su kuma a matsayinta na mai ba da shawara a Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Amurka ta shekarar 2021 na Annobar cutar COVID-19 da Big Data.[13]
Kyaututtuka da karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]Oladipo ta kasance Masaniya (Faculty Scholar) a Kwalejin Grace Hopper, kuma a cikin shekarar 2016 an karrama aikinta na koya wa 'yan mata matasa game da lafiyar haihuwa ta hanyar aikace-aikacen wayar hannu na ilimi (Educational Mobile Application).[14] A cikin shekarar 2020, Oladipo tana ɗaya daga cikin mutane 18 da aka ambata a matsayin ƙwararrun ƴan ƙungiyar Kwamfuta ta Najeriya.[15]
Zaɓaɓɓun wallafe-wallafe
[gyara sashe | gyara masomin]- Awoleye, Michael Olusesan; Siyanbola, Willie Owolabi; Oladipupo, Onaolapo Francisca (20 April 2008). "Adoption Assessment of Internet Usage Amongst Undergraduates In Nigeria Universities -A Case Study Approach". Journal of Technology Management & Innovation. 3 (1): 84–89. ISSN 0718-2724.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Campus Connect. "Professor Francisca Oladipo Appointed as the Pioneer Director of Quality Assurance, FUL". campusconnect.com.ng. Retrieved April 8, 2020.[permanent dead link]
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "VODANA Executive Secretary, Prof Francisca Oladipo appointed as the Pioneer Director of Quality Assurance, Federal University Lokoja, Nigeria". www.vodan-totafrica.info (in Turanci). VODAN Africa & Asia. Retrieved 2022-01-15.
- ↑ Campus Connect. "Professor Francisca Oladipo Appointed as the Pioneer Director of Quality Assurance, FUL". campusconnect.com.ng. Retrieved April 8, 2020.[permanent dead link]
- ↑ fulokoja. "Francisca Onaolapo Oladipo". fulokoja.edu.ng. Retrieved March 26, 2020.
- ↑ "Oladipo". Africa Scientists Directory. Retrieved 8 April 2021.
- ↑ Jessica Fjimori. "A new leadership cadre for science and engineering". MIT News. Retrieved April 8, 2020.
- ↑ Oredola, Tayo (2017-02-08). "Total, MIT, others task NUC on human capacity building". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Retrieved 2022-03-05.[permanent dead link]
- ↑ PyCon Clevaland 2019. "Francisca Onaolapo Oladipo". us.pycon.org. Retrieved April 8, 2020.
- ↑ "Presentation: Implementing a Chatbot for Positive Reinforcement in Young Learners | PyCon 2019 in Cleveland, Ohio". us.pycon.org. Retrieved 2022-01-15.
- ↑ Agbo, Friday Joseph; Oyelere, Solomon Sunday; Suhonen, Jarkko; Laine, Teemu H. (2021-09-01). "Co-design of mini games for learning computational thinking in an online environment". Education and Information Technologies (in Turanci). 26 (5): 5815–5849. doi:10.1007/s10639-021-10515-1. ISSN 1573-7608. PMC 8097249 Check
|pmc=
value (help). PMID 33967590 Check|pmid=
value (help). - ↑ "Contribution to the panel discussions at the First Session of the Intergovernmental Preparatory Committee for LDC5" (PDF). United Nations. May 20, 2021. Retrieved January 15, 2022.
- ↑ Reisen, Mirjam; Oladipo, Francisca; Stokmans, Mia; Mpezamihgo, Mouhamed; Folorunso, Sakinat; Schultes, Erik; Basajja, Mariam; Aktau, Aliya; Amare, Samson Yohannes; Taye, Getu Tadele; Purnama Jati, Putu Hadi (2021). "Design of a FAIR digital data health infrastructure in Africa for COVID‐19 reporting and research". Advanced Genetics (in Turanci). 2 (2): e10050. doi:10.1002/ggn2.10050. ISSN 2641-6573. PMC 8420285 Check
|pmc=
value (help). PMID 34514430 Check|pmid=
value (help). - ↑ "Data-Informed Societies Achieving Sustainability: Tasks for the Global Scientific, Engineering, and Medical Communities: A Virtual Workshop". www.nationalacademies.org. September 2021. Retrieved 2022-01-15.
- ↑ Tech Women (25 October 2016). "GRACE HOPPER CELEBRATION UNITES FELLOWS AND MENTORS IN HOUSTON". techwomen.org. Retrieved April 8, 2020.
- ↑ "ANNUAL GENERAL REPORTS 2020" (PDF).
- Haihuwan 1978
- Rayayyun mutane
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from December 2023
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- CS1 Turanci-language sources (en)
- Articles with dead external links from January 2024
- CS1 errors: PMC
- CS1 errors: PMID