Funminiyi Afuye
Appearance
Funminiyi Afuye | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Shekarun haihuwa | 1956 |
Lokacin mutuwa | 19 Oktoba 2022 |
Sana'a | ɗan siyasa |
Funminiyi Afuye (ranar 11 ga watan Yulin 1956 - ranar 19 ga watan Oktoban 2022) ɗan siyasar Najeriya ne kuma lauya.[1][2][3][4][5] Ya kasance kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Ekiti kuma ɗan majalisar jihar Ekiti sau biyu mai wakiltar mazaɓar Ikere I.[5][6][7]
Ofisoshin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Funminiyi Afuye ya kasance memba na majalisa ta uku tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.[8][1] Daga 2011 zuwa 2014, ya kasance Kwamishinan ma’aikatu guda biyu; Ma'aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Ekiti da Ma'aikatar Haɗin Kai da Harkokin Gwamnati a zamanin Gwamna Kayode Fayemi.[9][10] An sake zaɓen shi a majalisa ta shida kuma ya zama kakakin majalisa a ranar 6 ga watan Yunin 2019.[11]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 https://punchng.com/breaking-ekiti-speaker-afuye-dies-at-66/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/more-news/560523-ekiti-assembly-speaker-funminiyi-afuye-is-dead.html?tztc=1
- ↑ https://gazettengr.com/ekiti-speaker-congratulates-muslims-on-eid-el-fitr-celebration/
- ↑ https://www.sunnewsonline.com/ekiti-east-by-election-winner-fatoba-sworn-in-as-member-of-house-of-assembly/
- ↑ 5.0 5.1 https://tribuneonlineng.com/ekiti-assembly-speaker-afuye-dies-at-66/
- ↑ https://www.channelstv.com/2022/10/19/just-in-ekiti-state-house-of-assembly-speaker-is-dead/amp/
- ↑ https://www.legit.ng/nigeria/1498849-ekiti-house-assembly-speaker-funminiyi-afuye-dies-illness/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-11-05. Retrieved 2023-04-04.
- ↑ https://saharareporters.com/2022/10/19/breaking-ekiti-house-assembly-speaker-afuye-dead
- ↑ https://thenationonlineng.net/afuyes-house-of-banter/
- ↑ https://pmnewsnigeria.com/2022/10/19/breaking-ekiti-speaker-afuye-in-sudden-death/