Jump to content

Gurara Waterfalls

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gurara Waterfalls
General information
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 9°18′52″N 7°01′16″E / 9.314319°N 7.021069°E / 9.314319; 7.021069
Bangare na Abuja
Wuri Gurara
Kasa Najeriya
Territory Jihar Neja

Gurara Waterfalls Yana cikin Gurara, karamar hukumar Jihar Neja, Arewa ta Tsakiyar Najeriya.[1] Magudanar ruwan tana da tsayin kusan mita 30 kuma tana kan kogin Gurara da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna.

Labarin tarihin Wajen

[gyara sashe | gyara masomin]

Kamar yadda tarihi ya nuna cewa wani mafarauci ne da ake kira da suna Buba ya gano magudanar ruwan na Gurara a shekarar 1745 kafin wasu Turawa su gano shi a shekarar 1925 bayan sun same shi a matsayin wurin shakatawa . Kafin gano magudanan ruwa da Turawa suka yi, Guara Waterfalls ya kasance wajen bautar mutanen da ke zaune a kewayen shi. Har ila yau, tarihin baka ya nuna cewa, Gurara Waterfalls da Kogin Gurara suna da sunan gumaka guda biyu da ake kira da suna Gura da Rara. wanda daga baya saka hade su a waje daya shine ya bada (gurara).

Yawon shakatawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Duk da tarihin da aka bincika, Gurara Waterfalls na ɗaya daga cikin manyan wuraren yawon buɗe ido a Najeriya. A baya-bayan nan an yi shirin mayar da shi wurin shakatawa da seven-star hotel a kewaye da shi.

  • Jerin magudanun ruwa
  1. Premium Times (2016-04-18). "Travelogue: Gurara Waterfall: A premium Nigerian picnic hotspot - Premium Times Nigeria". Premiumtimesng.com. Retrieved 2017-06-10.