Hamisu Musa
Hamisu Musa | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Sana'a |
Hamisu Musa ɗan siyasan Najeriya ne kuma mai gudanar da mulki wanda ya kasance ministan ma'aikatar gidan waya daga watan Oktoba shekara ta1983 zuwa watan Disamba shekara ta 1983. Ya kuma kasance sanata mai wakiltar Kano ta Kudu maso Yamma a lokacin jamhuriya ta biyu ta Nijeriya. Yayin da yake majalisar dattijai, ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin cigaban zamantakewar jama'a. [1]
Ya taka muhimmiyar rawa a zaben Rabiu Kwankwaso a zaben fidda gwani na PDP a shekara ta 1998 tare da Musa Gwadabe da Abdullahi Aliyu Sumaila wadanda suka kasance shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Movement (PDM) daga inda Rabiu Musa Kwankwaso ya fito takarar fitar da gwani inda ya kayar da Abdullahi Umar Ganduje . Musa tsohon shugaban bankin Arewa ne da kuma Kamfanin bada kwangila na Najeriya Express. An haife shi a Kafir Agur, Kano a shekara ta 1938 kuma yayi karatun sa a New York Institute of Management. A shekara ta 1979, ya kayar da Muhammadu Maude na NPN don lashe kujerar sanata na yankin kudu maso yamma na Kano karkashin inuwar Jam’iyyar Redemption Party.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Feinstein, Alan. African Revolutionary, the life and times of Nigeria's Aminu Kano.
- ↑ Afolabi, Micheal (1980). Nigeria in Transition, 1978-1979: An Annotated Bibliography of Party Politics, Elections, and the Return to Civil Rule. Department of Library Science, Ahmadu Bello University, 1980.