Hannatu Bashir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hannatu Bashir
Rayuwa
Haihuwa Kano, 2 Oktoba 1992 (31 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Jarumi
Hannatu a yayin shirin fim

Hannatu Bashir (an haife ta a ranar 2 ga watan Octoba shekara ta alif ɗari tara da cassain da biyu 1992A.c). kuma ta girma a jihar Kano, yankin arewa maso yammacin Najeriya. Hannatu ta kammala karatun NCE ne a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, jihar Kano.

Hannatu Bashir Da akafi sani da Hanan ta shiga masana’antar fina-finan Hausa, Kannywood ne a shekara ta 2012 ta hanyar taimakon Marigayi Umar Jalo, wanda abokin kawun ta ne. Ta ce tun daga shekara ta 2012 lokacin da ta shiga masana'antar, ta samu kwangila tare da MTN don yin tallar da aka biya ta kuma tun daga wannan lokacin take ta tashi tare da samun cikakken aiki tare da Rite Time Multimedia. Fitacciyar Jarumar Kukan Kurciya ta lura cewa a shekarunta na yanzu akwai aiki a gabanta domin har yanzu ba ta tabbatar da kimarta a cikin Masana'antar ba duk da cewa ta samu daga masana'antar. Jerin talabijin mai taken: "Kukan Kurciya" game da tsohuwar al'ada ce da ke nuna yadda al'ummomin yankin ke yakar junan su akan filaye, shanu, mata, kogi ko wuraren masana'antu. Hannatu ta kuma taka rawar gani a wasu finafinai na Hausa.

Fina Finan ta na Kannywood[gyara sashe | gyara masomin]

(BT) na nufin Ba Tabbas, ma'ana babu tabbacin kwanan wata da shekarar da fim din ya fita. Yayin da akwai wasu kuma da ake da tabbacin kwanan watan fitar su.

Fim ↑ Shekara
Hindu BT
Dare Biyu BT
Mairo BT
Makauniya BT
Kukan Kurciya BT

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://www.blueprint.ng/abuja-journalists-declare-7-day-mourning-for-late-chair/