Hari a Agbudu
Iri | aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 29 ga Yuli, 2020 |
Wuri | Jahar Kogi |
Ƙasa | Najeriya |
Adadin waɗanda suka rasu | 14 |
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 6 |
Harin Agbudu hari ne da aka kai ranar 29 ga watan Yuli, 2020 a ƙauyen Agbudu, jihar Kogi, Najeriya.[1] Harin ya yi sanadin mutuwar mutane 14 tare da jikkata wasu 6. 13 daga cikin waɗanda suka mutun ƴan gida ɗaya ne. Ƴan sanda sun ce ana zargin cewa an daɗe ana takun saka a kan hakkin mallakar fili ne ya haddasa harin.[2]
Lamarin
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 29 ga Yuli, 2020, wasu gungun ƴan bindiga a saman babura sun buɗe wuta kan al’umma a jihar Kogi, Najeriya, inda suka kashe mutane 14, in ji ‘yan sanda.[3] A cewar shugaban rundunar ‘yan sandan jihar, Ede Ayuba, 13 daga cikin waɗanda abin ya shafa ‘yan ƙabilar Agbudu ne a karamar hukumar Korton-Karfe a jihar Kogi.[4] Wasu 6 sun jikkata a harin kuma maharan ba a san ko su wanene ba. Har yanzu dai babu tabbas kan musabbabin harin, ‘yan sandan sun ce wata kila rikicin filaye da aka dade ana yi shi ne dalilin harin.[3] An aika da jami’an tsaro zuwa yankin kuma an ƙaddamar da bincike kan ko suwaye maharan unji Ayuba. Harin dai na zuwa ne biyo bayan dokar hana hawa babura da wasu jihohi suka fara yi a matsayin martani ga amfani da su a hare-haren baya-bayan nan.[5][6]
Martani
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan harin, shugaban ‘yan sandan jihar Ede Ayuba ya shaida wa manema labarai cewa “karamar hukumar da dukkan ma’aikata suna taimaka mana” sannan “Ohimege, Alhaji Abdulrazaq Isa-Koto shi ma ya taimaka mana.”[7]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Gunmen kill family of 13 in Kogi State". The Guardian (Nigeria). 30 July 2020. Archived from the original on 1 August 2020. Retrieved 30 July 2020.
- ↑ "14 killed in attack on village in central Nigeria". Al Jazeera English. 30 July 2020. Retrieved Jul 30, 2020.
- ↑ 3.0 3.1 "Nigeria: Gunmen kill 14 in attack in Kogi state July 28". GardaWorld. Archived from the original on 2020-11-27. Retrieved 2020-08-11.
- ↑ "14 killed by gunmen in central Nigeria attack - Xinhua | English.news.cn". Xinhua News Agency. Retrieved 2020-08-11.
- ↑ "Nigeria: Gunmen on motorcycles kill 14 villagers". Anadolu Agency. Archived from the original on 31 July 2020.
- ↑ "14 killed by gunmen in central Nigeria attack - China.org.cn". www.china.org.cn. Retrieved 2020-08-11.
- ↑ "Gunmen shoot family of 13 dead in Kogi". P.M. News (in Turanci). 2020-07-29. Retrieved 2020-08-11.