Hari a Bakura da Talata Mafara
Iri | aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 28 ga Maris, 2022 |
Wuri |
Bakura (Nijeriya) Talata-Mafara |
Ƙasa | Najeriya |
Wanda ya rutsa da su | biyar |
Tsakanin ranar 28 ga Maris zuwa 30 ga Maris, 2022, 'yan bindiga sun kai hari a kauyukan Bakura da Talata Mafara a jihar Zamfara, Najeriya, inda suka kashe mutane da dama, ciki har da hakimin kauyen 'Yargeda.
Gabatarwa
[gyara sashe | gyara masomin]A duk fadin jihar Zamfara, ana fama da rikici tsakanin fararen hula, sojojin Najeriya, da kungiyoyin 'yan bindiga akalla 100 daban-daban.[1] Wata kungiya mai suna Katare ita ce mafi girma kuma mafi muni a kananan hukumomin Bakura da Talata Mafara na jihar Zamfara. [2] Wani hari da ‘yan bindiga suka kai a watan Janairun 2022 a karamar hukumar Anka, ya kashe mutane 200, wanda shi ne mafi muni a jihar. 'Yan fashin Katare da yawa suna zaune a ƙauyen Katsalle, wanda ba shi da nisa da wuraren da aka kai hari ranar 30 ga Maris.[2]
Kisan gilla
[gyara sashe | gyara masomin]An fara kai hare-hare na farko ne a ranar 28 ga Maris, lokacin da ‘yan bindigar Katare suka kai hari a kauyukan Ruwan Gizo, Ruwan Gora, Boraye, da Dajin Banza a Talatan Mafara. An yi garkuwa da mutane da dama a hare-haren, kuma an kashe tsohon mataimakin shugaban majalisar Talata Mafara a harin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa da misalin karfe 11:45 na dare ‘yan Katare sun far wa kauyukan Ruwan Gizo da Ruwan Gora da ke karamar hukumar Talata Mafara da kuma kauyen ‘Yargeda da ke karkashin karamar hukumar Bakura a kan babura, inda suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili.[3] Kimanin 'yan fashi 100 ne suka shiga, kuma suka toshe duk wata hanyar fita zuwa garin. An kashe shugaban ‘Yargeda Abdu Umuru ne tare da wasu mutane uku bayan ‘yan bindigar sun kai farmaki gidansa tare da harbe duk wanda ke cikin gidan. [3] Shugaban Talatan Mafara, Aminu Sulaiman, ya kira sansanin sojojin Najeriya da ke yankin domin neman agaji a lokacin harin amma babu wanda ya dauki wayar.[4] Ba a iya tantance adadin mutanen da aka kashe a lokacin saboda mutane da dama sun tsere cikin daji. [3] An kuma yi garkuwa da mutane da dama, kuma an kawo karshen harin da karfe 2:15 na safe. [2]
Bayan haka
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan harin, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bukaci mazauna yankin da su kare kansu daga ‘yan bindigar. Garuruwan sun samu ziyarar ne ta hannun mataimakin gwamnan jihar Hassan Nasiha, inda ya jajantawa. [3] Rundunar ‘yan sandan yankin dai ba ta ce uffan ba kan hare-haren, kuma ta bukaci fararen hula da su kira sojoji idan aka sake kai musu hari.
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "30,000 bandits terrorizing my state, says Gov Matawalle". The Nation. April 3, 2021. Retrieved September 12, 2023.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Abubakar, Abdullahi (2022-03-31). "Zamfara Governor Tells Locals To Fight Back After Terrorists Kill Village Head, 3 Others". HumAngle (in Turanci). Retrieved 2023-09-12.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 www.premiumtimesng.com https://www.premiumtimesng.com/regional/nwest/521054-bandits-attack-zamfara-communities-kill-several-people-including-village-head.html?tztc=1. Retrieved 2023-09-12. Missing or empty
|title=
(help) - ↑ Ladd, Brian (March 31, 2022). "Bandits Assault Ruwan Gora and Ruwan Gizo villages in Talata Mafara LGA and Yar Geda village in Bakura LGA, Zamfara State, Nigeria". Terrorism Research and Analysis Consortium (TRAC). Retrieved September 12, 2023.