Hari a Buni Yadi, Mayu 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHari a Buni Yadi, Mayu 2014
Map
 11°16′08″N 11°59′49″E / 11.2689°N 11.9969°E / 11.2689; 11.9969
Iri faɗa
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 27 Mayu 2014
Adadin waɗanda suka rasu 58
Buni yadi news

Harin Buni Yadi na watan Mayun 2014 wani harin ta'addanci ne da ya faru a ranar 27 ga watan Mayun 2014 a garin Buni Yadi na jihar Yobe a Najeriya.[1][2] An kashe wasu jami'an tsaro 49 (sojoji da ƴan sanda),da fararen hula 9.[3][4][5]

An ɗora alhakin kai harin akan ƴan kungiyar Boko Haram.[6][7]

Masomi[gyara sashe | gyara masomin]

Rikicin Boko Haram na tada ƙayar baya, daga ƙungiyar ta Boko Haram. Ya soma ne a shekara ta 2009 a kan gwamnatin Najeriya, amma ya faɗaɗa zuwa kai hari ga wasu jihohi.[8]

Kai hari[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin kai harin, mahara da dama ne suka taru a wajen garin da sukayi badda kama cikin wata mota ƙirar Toyota Hilux ɗauke da bama -bamai haɗi da makaman roka. Da misalin karfe 8:00 na UTC, ƴan ta'addan sun kai hari a wani shingen binciken sojoji, inda suka yi ta harbe-harbe kan sojojin da ke wurin. Sannan kuma sun kona ofishin ‘yan sandan yankin tare da kashe ‘yan sandan ciki har da jami’in ‘yan sandan shiyya. An kuma kona wasu gine-ginen gwamnati da dama tare da gidan wani shugaban karamar hukumar. Mayakan sun kai farmaki kan wata makarantar firamare da babu kowa. A cewar wani ganau, maharan sun nufi jami’an tsaro ne, maimakon farar hula. Mutuwar farar hula ta zama kamar ba da gangan ba. An kawo karshen harin da misalin karfe 9:00 a agogon UTC.[1][3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "24 personnel feared killed as Boko Haram attacks military,police base" Archived 2016-03-04 at the Wayback Machine, Nigerian Monitor, Wednesday, 28 May 2014.
  2. "Boko Haram Kills 14 Top Soldiers, Police DPO In Latest Attack", Archived 19 ga Augusta, 2014 at the Wayback Machine By ireport, Citypeoplenews.com on 27 May 2014.
  3. 3.0 3.1 "Soldiers, Police Killed In Boko ‘Revenge’ 4 Hours Terror In Yobe, Borno", NewsRescue, Wednesday, 28 May 2014.
  4. "Boko Haram gunmen kill 24 soldiers, 21 police officers", Archived 19 ga Augusta, 2014 at the Wayback Machine Nigerian Tribune, 27.May.2014.
  5. "Boko Haram attacks police station, army base…kills 40 soldiers, policemen in Yobe", Archived 29 Mayu 2014 at the Wayback Machine 28 May 2014 by Kayode Idowu, Punch (Nigeria).
  6. "Nigerian security services hit in fresh Boko Haram attack", The Telegraph, 8:09PM BST, 27 May 2014.
  7. "Military, police hit in fresh Boko Haram attack", Worldnews.com, 27 May 2014.
  8. "Who are Nigeria's Boko Haram Islamist group?". BBC News. 24 November 2016. Retrieved 20 July 2022.

Coordinates: 11°16′08″N 11°59′49″E / 11.2689°N 11.9969°E / 11.2689; 11.9969