Jump to content

Harin Jirgin Sama na Kwatar Daban Masara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harin Jirgin Sama na Kwatar Daban Masara
airstrike (en) Fassara
Bayanai
Kwanan wata 26 Satumba 2021
Wuri
Map
 12°48′17″N 13°50′16″E / 12.8048°N 13.8379°E / 12.8048; 13.8379

Harin jirgin saman Daban Masara ya afkawa kasuwar kifi a ƙauyen Kwatar Daban Masara, jihar Borno, Najeriya a ranar 26 ga Satumba, 2021, inda ya kashe mutane tsakanin 50 zuwa 60.[1]

Kwanaki 10 gabanin kai harin ta sama mayaƙan ƙasashen waje na ISWAP sun isa Kwatar Daban Masara a cikin manyan motoci. Hakan ya sa jami'an leken asirin Najeriya suka sanyawa garin sa ido .

A ranar 26 ga Satumba, 2021, sojoji sun sami majiyar cewa ISWAP na shirin kai hari daga garin. Sojojin saman sun yanke shawarar ɗaukar matakin ne da misalin karfe 6:00 na safe agogon kasar, wani jirgin saman sojan sama ya kai wani hari na riga-kafi a kasuwar kifi da ke ƙauyen, inda ya kashe fararen hula akalla 50-60.[2][3]

  1. "Nigerian air force kills dozens of civilians in northeast - sources". reuters. 28 September 2021. Retrieved 28 September 2021.
  2. "Nigeria Air Strike Kills 20 Fishermen: Sources". thedefensepost. 28 September 2021. Retrieved 28 September 2021.
  3. "Nigeria air strike kills 20 fishermen". borneobulletin. 29 September 2021. Archived from the original on 29 September 2021. Retrieved 29 September 2021.