Jump to content

Hawan daba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
hawan daba
Hawan Daba
Hawan Daba
Hawan daba

Hawan Daba Bikin Hawan Daba sabon biki ne a ƙasar Hausa.[ana buƙatar hujja] Sabon biki a nan yana nufin ba biki ne na tun ɗauri ba, wanda Bahaushe ya gada tun kaka-da-kakanni, biki ne da ya shigo ƙasar Hausa bayan zuwan Turawa.[1]

Ana bikin Hauwan Daba ne don sada zumunci tsakanin sarakuna ko kuma tarbar wani baƙo.

A wannan biki na Daba sarakuna kan haɗu da su da hakimansu, kowane ɗaya da tawagarsa su hau dawakai. Za a caɓa musu ado.

Ana gudanar da wannan biki na Daba a filin da yake da faɗiso sai. Waɗancan tawagogi na sarakuna waɗanda suke mahaya dawakai, za su rika zuwa suna kewayowa sannan su zo gaban Babban sarki su kawo caffa ko kuma anyi babban baƙon da ake karramawa da wannan biki na Hawan Daba.

Wannan biki na Hawan Daba wata hanya ce ta ƙulla zumunci tsakanin sarakuna da kuma nuna wa Baƙon da ake karramawa daɗaɗɗiyyar al'adar da Bahaushe yake da ita.

An gudanar da Hawan Daba na farko a arewacin Najeriya a cikin shekarar 1975 a garin Kaduna domin karramawa sarauniyar Ingila.[ana buƙatar hujja]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-22. Retrieved 2022-10-22.