Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Edo
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Edo | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | government organization (en) , Lafiya da emergency (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Aiki | |
Bangare na | jahar Edo |
Harshen amfani | Turanci da Harshen Edo |
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Edo wata hukuma ce a Jihar Edo, Najeriya da ke da alhakin magance bala'o'i.[1] Hukumar tana ba da haɗin kai da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa don daidaita hanyoyin magance bala’o’i.[2] An sake fasalin hukumar ne a shekarar 2017 domin haɗa ta da sauran hukumomin tsaro a jihar tare da samar da hanyoyin tunkarar bala’o’i.[1][3]
Magance Ambaliyar Ruwa
[gyara sashe | gyara masomin]Hukumar tana daidaita yadda zata magance matsalar ambaliyar ruwa.[4][5] Bayan manyan ambaliyar ruwa da yawa, Hukumar ta fara ɗaukar matakan da suka dace dan yin aiki tare da ƙananan hukumomi dan hana ambaliya kafin aukuwar ambaliyar.[6]
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Edo ta kara da cewa ta yi isassun tsare-tsare don hana afkuwar ambaliyar ruwa tare da magance aukuwar lamarin. Daraktar ta, Mrs Carol Odion a Benin a ranar Larabar da ta gabata cewa hukumar ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a a kananan hukumomi 18 na jihar kan ambaliyar ruwa. Ta ce hukumar ta kuma gina matsugunai na wucin gadi ga ‘yan gudun hijirar (IDP) kafin a kai daukin gaggawa.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Toriola, Olajide (2017-04-13). "Edo Re-jigs State Emergency Management Agency for Proactive Response". Western Post News (in Turanci). Archived from the original on 2021-10-02. Retrieved 2021-10-02.
- ↑ Toriola, Olajide (2017-04-13). "Edo Re-jigs State Emergency Management Agency for Proactive Response". Western Post News (in Turanci). Archived from the original on 2021-10-02. Retrieved 2021-10-02.
- ↑ "Edo reforms state emergency mgt agency for proactive response". Vanguard News (in Turanci). 2017-04-12. Retrieved 2021-10-02.
- ↑ Lashem, Favour (2021-09-01). "Edo set to contain flooding". Newsdiaryonline (in Turanci). Retrieved 2021-10-02.
- ↑ "Flood ravages Benin City, renders many homeless". Vanguard News (in Turanci). 2020-06-22. Retrieved 2021-10-02.
- ↑ Emeka, Ifeanyi (2021-09-07). "Edo SEMA maps out plans to mitigate flooding". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2021-10-02.
- ↑ https://thisnigeria.com/edo-set-to-contain-flooding/