Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano |
---|
Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) hukuma ce da aka kafa a shekarar 2005 domin yaki da cin hanci da rashawa da kuma warware korafe-korafen al’umma a Jihar Kanon Najeriya . PCACC tana da wa'adi biyu na yin aiki a matsayin mai shigar da ƙara da kuma ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashawa.[1][2][3]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Majalisar Dokokin Jihar Kano ce ta kafa PCACC a shekarar 2005, bayan kafa dokar Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano a shekarar 2005. An gyara dokar a cikin 2008 da 2016 don ƙarfafa iko da ayyuka na PCACC. PCACC kungiya ce mai zaman kanta wacce ba ta karkashin iko ko shugabanci ko wani mutum ko wata hukuma, sai Gwamnan Jihar Kano wajen yin amfani da ikonsa na tsarin mulki.[4][5]
Hukumar ta PCACC dai tana karkashin jagorancin shugaban zartaswa ne, wanda gwamnan jihar Kano ne ke nada shi tare da amincewar majalisar dokokin jihar Kano. Shugaban zartaswa yana da kwamishinoni hudu ne ke taimaka wa, wadanda ke da alhakin gudanarwa, bincike, gabatar da kara, da kuma wayar da kan jama'a. Muhuyi Magaji Rimin Gado shine shugaban riko na hukumar PCACC, wanda aka nada a shekarar 2015.[6][7][8]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- EFCC
- ICPC
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kano state government adopts anti-corruption strategy". Justice, conflict and security in Nigeria. December 20, 2020.
- ↑ "WPS 365". eu.docs.wps.com. Retrieved 2024-01-25.
- ↑ "About PCACC". Public Complaints and Anti-Corruption Commission (in Turanci). Retrieved 2024-01-25.
- ↑ "Kano State Public Complaints and Anti-Corruption Commission Archives". Peoples Gazette Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-01-25.
- ↑ "Hukumar Karbar Korafe-Korafe Ta Jihar Kano". All News Hausa.
- ↑ "Wane ne Muhuyi Magaji Rimin Gado?". BBC News Hausa. Retrieved 2024-01-25.
- ↑ "Governor Abba Kabir Reinstates Barr. Muhuyi Magaji as Kano Anti Corruption Boss - Nigerian Television Authority --Africa's Largest TV Network". nta.ng (in Turanci). 2023-06-21. Retrieved 2024-01-25.
- ↑ Odogwu, Ted (2023-08-28). "Kano committed to anti-corruption war despite criticism, says anti-graft boss". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-01-25.