Ibrahim Abubakar Njodi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ibrahim Abubakar Njodi (an haife shi a watan Janairu a shekara ta alif dari tara da hamsin da tara (1959). [1] Farfesa ne aɓangaren ilimin kiwon lafiya, ɗan Najeriya kuma tsohon mataimakin shugaban jami'ar Maiduguri.[2][3][4] Gwamna Inuwa Yahya ya naɗa Farfesa Ibrahim Njodi a matsayin sakataren gwamnatin jihar Gombe nan da nan bayan wa’adinsa ya cika a matsayin mataimakin shugaban jami’ar Maiduguri.[5]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Ibrahim Abubakar Njodi ya yi makarantar firamare ta L.E.A da ke Kaltungo daga 1967 zuwa 1973, sannan ya yi makarantar firamare ta ECWA a Kaltungo daga 1973 zuwa 1975. Daga 1975 zuwa 1980 ya halarci kwalejin malaman gwamnati da ke Jama’are a jihar Bauchi. Ya yi digirinsa na farko a fannin lafiya acikin shekarar ta 1985, daga Jami’ar Maiduguri. Daga baya, daga 1988 zuwa 1991, ya yi digirinsa na biyu a fannin ilmin kiwon lafiya a wannan jami'a. Daga 2000 zuwa 2003, ya yi karatun Ph.D. a fannin ilimin kiwon lafiyar jama'a a shahararriyar jami'ar Najeriya, Nsukka.[6][7]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya shiga aikin gwamnati ne a matsayin graduate assistant a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1987. Njodi ya rike mukamin shugaban tsangayar ilimi na jami'ar daga 2008 zuwa 2010, sannan ya zamo Mataimakin Shugaban Jami'ar daga Yuni 2014 zuwa Yuni 2019.[8][6] A halin yanzu Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi shine sakataren gwamnatin jihar Gombe (SSG) na jihar Gombe.[9]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]