Jump to content

Idewu Ojulari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Oba Idewu Ojulari (ya rasu c 1835) yayi sarautar Oba na Legas daga 1829 zuwa misalin 1834/5. Mahaifinsa, shi ne Oba Osinlokun da ’yan'uwansa Kosoko (wanda shi ne Oba daga 1845 zuwa 1851) da kuma Opo Olu,mace mai arziki kuma mai rike da baiwa.

Idewu Ojulari ya kashe kansa

[gyara sashe | gyara masomin]

Idewu Ojulari ya zama Oba bayan mahaifinsa Osilokun ya rasu a 1829. Duk da haka, mulkin Idewu Ojulari bai samu karbuwa ba,kuma bisa umarnin Oba na Benin,wanda mutanen Legas suka kai kara,Idewu Ojulari ya kashe kansa. Musamman ma,Legas ta kasance a karkashin Benin har zuwa lokacin mulkin Oba Kosoko wanda sojojin Birtaniya suka tumbuke a 1851. Bayan haka,Oba Akitoye da magajinsa,Oba Dosunmu,sun ki amincewa da biyan harajin shekara-shekara ga Benin.

A cewar masanin tarihi Kristin Mann, rashin farin jinin Idewu Ojulari na iya faruwa ne sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin da ake samu a cinikin bayi bayan shekaru masu albarka na mulkin Osinlokun.Rahotanni sun ce sarakunan Idewu sun bayyana rashin jin dadinsu ga Oba na Benin, wanda ya aika wa Idewu kokon kai,da takobi,da sakon cewa “mutanen Legas ba za su kara gane shi a matsayin Sarkinsu ba.Idewu ya gane kwanyar a matsayin gayyata don ɗaukar guba da takobi a matsayin kiran yaƙi.Idewu ya dauki zabin guba ya kashe kansa.