Jump to content

Idris Waziri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Idris Waziri
Minister of Commerce and Industry (en) Fassara

ga Yuli, 2003 - ga Yuni, 2006 - Aliyu Modibbo Umar
Rayuwa
Haihuwa Jahar Taraba, 12 Oktoba 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Ambasada Idris Waziri ya jagoranci ma’aikatar kasuwanci ta tarayyar Najeriya, daga shekarar 2003 zuwa watan Yunin 2006 lokacin da ya yi murabus daga mukaminsa ya tsaya takara a zaben gwamnan jihar Taraba a shekarar 2007. Gwamnan jihar Taraba Arc Darius Ishaku ne ya nada shi a matsayin Pro Chancellor/Chairman Governing Council na jami’ar jihar Taraba a shekarar 2021.[1]

karatu da Aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Waziri ya yi digiri a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya Kuma koma cikin gwamnati a matsayin jami’in gudanarwa.[ana buƙatar hujja], ya zama Sakatare na dindindin sannan kuma Kwamishinan Kudi, Kasuwanci da Masana'antu, ya yi ritaya a 1993.[ana buƙatar hujja] sannan yayi aiki a masana'antu masu zaman kansu.[ana buƙatar hujja]Ya kasance memba peoles Democratic Party (PDP)[ana buƙatar hujja]A cikin 1999 Obasanjo ya nada shi Jakadan Najeriya a Pakistan.[ana buƙatar hujja] an nadashi a matsayin Ministan Kasuwanci a watan Yuli 2003. A shekarar 2021 Gwamnan jihar Taraba Arc Darius Dickson Ishaku ne ya nada shi a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na jami’ar jihar Taraba.[2]

Takarar Gwamna

[gyara sashe | gyara masomin]

Waziri ya tsaya takarar gwamnan jihar Taraba a shekarar 2007 bai samu nasara ba, a shekarar 2013 Dan-Baba Suntai a ya zabe shi don ya tsaya takarar shugaban jam’iyyar PDP na kasa. A ranar 3 ga Yuni, 2021, aka rantsar da Waziri a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na jami'ar jihar Taraba

A lokacin da yake rike da mukamin ministan kasuwanci, Waziri yana yawan fitar da rogo zuwa kasashen waje domin kasuwanci.[3]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-29. Retrieved 2022-10-29.
  2. https://citizensciencenigeria.org/public-offices/persons/idris-waziri/
  3. https://www.zgr.net/en/people/idris-waziri-biography-fact-career-awards-net-worth-and-life-story/

Samfuri:Cabinet of President Olusegun Obasanjo 2003-2007