Islamic feminism
mata na Islama wani nau'ine na mata dake damuwa da rawar mata a Islama.Yana da niyyar cikakken daidaito na dukkan Musulmai, ba tare da la'akari da jinsi ba'a rayuwar jama'a data sirri.'Yan mata na Islama suna bada shawara ga haƙƙin mata, daidaito tsakanin jinsi,da kuma Adalci na zamantakewa wanda aka kafa acikin tsarin Islama. Kodayake sun samo asaline daga addinin Islama,masu gabatarwa na motsi sun kuma yi amfani da maganganun mata na duniya, na Yamma, ko kuma wadanda ba Musulmai ba, kuma sun fahimci rawar da mata na Islama ke takawa a matsayin wani ɓangare na hadin gwiwar mata na duniya.
Masu bada shawara na motsi suna neman nuna koyarwar daidaito acikin addini, kuma suna ƙarfafa yin tambaya game da fassarorin shugabanci na Islama ta hanyar sake fassara Alkur'ani da kuma Hadisi.
Shahararrun masu tunani sun hada da Begum Rokeya, Amina Wadud, Leila Ahmed, Fatema Mernissi, Azizah al-Hibri, Riffat Hassan, Asma Lamrabet, da kuma Asma Barlas.