James Moorhouse (ɗan siyasa)
Cecil James Olaf Moorhouse (1 Janairu 1924 - 6 Janairu 2014) ɗan siyasan Burtaniya ne kuma tsohon ɗan Majalisa a Tarayyar Turai. [1]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Yayi karatu a St Paul's School, London, King's College London (BSc Eng, 1945) da Imperial College Londo, inda a nan yayi difloma a fannin advanced aeronautics.[2]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Yayi aiki a matsayin ɗan majalisa a karkashin jam'iyyar Conservative na London ta Kudu daga 1979 zuwa 1984, kuma a matsayin MEP mai ra'ayin mazan jiya na London ta Kudu da Surrey East daga 1984 har zuwa Oktoba 1998 lokacin da "ya koma jam'iyyar Liberal Democrats bayan rashin yarda da manufofin Mr Hague kan kudin Euro ."[3]
Ya kasance a Majalisar Tarayyar Turai a matsayin MEP na Liberal Democrat na London ta Kudu da Surrey East har zuwa 1999.
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya mutu ranar 6 ga watan Janairu, 2014
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ James MOORHOUSE Obituary
- ↑ Dod's Parliamentary Companion. 1999.
- ↑ "MEPs quit 'euro-sceptic' Tory party". BBC News. 19 January 1999. Retrieved 15 November 2009.