Jump to content

Jamhuriya ta 4

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Jamhuriyya ta hudu fim ne na wasan kwaikwayo wanda ya shafi ɓangaren siyasa wanda akai a Najeriya a shekarar dubu biyu da goma sha tara 2019 wanda Ishaya Bako ya jagoranta kuma Ishaya Bako, Emil Garuba da Zainab Omaki suka rubuta. [1] It stars Kate Henshaw-Nuttal, Enyinna Nwigwe, Sani Muazu, Ihuoma Linda Ejiofor,[2] Bimbo Manuel, Yakubu Muhammed, Sifon Oko, Jide Attah, and Preach Bassey Produced by Amateur Heads and Griot Studios, 4th Republic ta samu tallafi daga John D. da Catherine T. MacArthur Foundation da kuma Open Society Initiative for West Africa (OSIWA) sun taru ne a kusa da wani mai neman takarar gwamna, Mabel King (Kate Henshaw) a sakamakon zaɓe na tashin hankali da magudi wanda ya haifar da mutuwar manajan yakin neman zabenta, Sikiru (Jide Attah). An nuna fim ɗin ne a jami'o'i bakwai da suke a Najeriya tare da hadin gwiwar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da Enough is Enough (EiE Nigeria) domin dakile tashe-tashen hankulan a lokacin zabe. Haka kuma hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta amince da fim ɗin.

Fim ɗin ya fara fitowa a Netflix a ranar 13 ga watan Yuni, na shekara ta dubu biyu da ashirin 2020.

Yin wasan kwaikwayo[gyara sashe | gyara masomin]

 

Production[gyara sashe | gyara masomin]

Jumhuriya ta 4 ta haɗin gwiwa ce tsakanin Amateur Heads da Griot Studios Ltd tare da Bem Pever, Ishaya Bako, Kemi 'Lala' Akindoju, da Ummi A. Yakubu a matsayin mai samarwa. Ishaya Bako, Emil Garuba da Zainab Omaki ne suka rubuta. Fim ɗin ya yi nazari ne kan jigogin tsarin siyasar Najeriya da ke ba da tarihin siyasa da tsarin zabe a cikin shekaru ashirin da suka gabata.

Saki[gyara sashe | gyara masomin]

An kaddamar da jamhuriya ta 4 a IMAX, Filmhouse cinemas a Lekki, Nigeria ranar 7 ga Afrilu, 2019. An sake shi a fadin gidajen sinima a Najeriya a ranar 9 ga Afrilu, bakin da suka halarci bikin sun hada da Sola Sobowale, Tope Oshin, Kehinde Bankole, Chigul, Waje, Lilian Afegbai, Denrele Edun, Japheth Omojuwa da Linda Osifo, da sauransu.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "'4th Republic' is a political thriller that sticks to the relatable facts". Pulse Nigeria (in Turanci). 2019-04-08. Retrieved 2020-06-14.
  2. "4th Republic premier stuns Lagos film denizens". The Sun Nigeria (in Turanci). 2019-04-12. Retrieved 2020-06-14.