Jami'ar Jihar Filato
Jami'ar Jihar Filato | |
---|---|
Knowledge, Diligence and Integrity | |
Bayanai | |
Iri | jami'a |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2005 |
plasu.edu.ng… |
Jami'ar Jihar Filato wata jami'a ce a Bokkos, Jihar Filato a Najeriya . An kafa ta a 2005. Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ce ta ba ta izini a ranar 29 ga Afrilu daidai da shekarar 2005 a matsayin Jami'a ta 66th a Nijeriya da kuma jihohi 24 da keda jami'a ta jiha cikin Kasar. An ambaci Dokar Tabbatar da Jami'ar a matsayin Dokar Mai lamba 4 ta 2005 (7 ga Maris, 2005) kamar yadda take a cikin Jihar Filato ta Nijeriya Gazette Mai lamba 3, Vol. 11 ga Mayu 24, 2006. Tana cikin Kauyen Diram tare da iyakar Butura-Tarangol a karamar hukumar Bokkos, kimanin kilomita 70 daga Jos babban birnin jihar Filato.
Kodayake ayyukan karatun sun fara ne a watan Mayu 2007 tare da ɗalibai 480, amma an dakatar da waɗannan ayyukan a ranar 10 ga Satumbar na wannan shekarar kuma ɗaliban suka koma Jami'ar Jos. An sake bude Jami'ar a watan Oktoban 2010 a lokacin Karatun Ilimin 2010/2011 tare da laccoci da suka fara a watan Janairun 2011.
</br>A watan Maris na 2016, Hukumar Kula da Jami'o'i ta ba da cikakken izini ga shirye-shirye 17 na farko a jami'ar. Wannan ya baiwa jami'ar matsayin "cikakkiyar jami'a".
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]https://web.archive.org/web/20160401074340/https://www.scholarsafrik.com/17-plateau-state-university-courses-accredited-by-nuc/ http://plasu.edu.ng/About-Us Archived 2021-04-11 at the Wayback Machine