Jamila Nagudu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jamila Nagudu
Rayuwa
Haihuwa 10 ga Augusta, 1985 (38 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo da Jarumi

Jamila Umar Nagudu (an haifeta a ranar 10 ga watan Agusta, a shekarata alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985). wacce aka fi sani da Jamila nagudu, ƴar wasan Kannywood ce ta Najeriya.[1][2]Jarumar ta yi fina -finai da dama irin su Indon ƙauye 2

Jamila da Jamilu

Tutar So

Matar Aure

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Jamila Nagudu a ranar 10 ga Agustan shekara ta 1985 a cikin garin Magana Gumau, ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi, Najeriya . Jamila ta yi makarantun firamare da sakandare a jihar Bauchi.[ana buƙatar hujja]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Jamila Umar wacce aka fi sani da Jamila Umar Nagudu ta fara fitowa a masana’antar Kannywood a shekara ta 2002. Tun lokacin da ta rabu, ta yanke shawarar fara fim. Ta bar Bauchi ta koma Kano ta gane cewa ta cimma burinta na zama jarumar fina-finai a masana'antar Kannywood. Ta kasance a harkar fim a matsayin mai rawa tun (2002). Sannan daga baya ta shiga harkar fim kaɗan kaɗan. Ƙoƙarin da ta yi a harkar nishadantarwa da wasan kwaikwayo ya jawo hankalin daraktoci har suka fara nuna ta a cikin fina-finansu. Jamila na iya fitowa a kowace rawa. Ta fito a fina-finan soyayya amma wani lokacin ma tana fitowa a fina-finan barkwanci. Nagudu ta yi fice sosai a Kannywood ta yadda ake yi mata lakabi da "Sarauniyar Kannywood". Darakta Aminu Saira shi ne ya fara jefa ta a fim din "Jamila da Jamilu" a matsayin jaruma.[3] An zabe ta a matsayin mafi kyawun Nollywood a Abeokuta.[4]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Jalima ta rabu da mijinta kuma tana da ɗa.[5][6] yaron ta a yanzu haka ya zama matashin saurayi, tayi aure da dama amma a yanzu haka bata da aure.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Tarihin Jaruma Jamila Umar Nagudu (Jamila Nagudu)". Haskenews-All About Arewa. Retrieved 2022-03-25.
  2. Adeleye, Kunle (2021-12-25). "Meet The Queen Of Kannywood, Jamila Umar Nagudu: Full Biography". Glamsquad Magazine (in Turanci). Retrieved 2022-03-25.
  3. "'Ibada da fim ne suka fi muhimmanci a wurina'". BBC News Hausa. 2018-04-04. Retrieved 2022-03-25.
  4. Online, Tribune (2017-09-16). "BON Awards: Jamila Nagudu, Omotola, others get nominations". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2022-07-28.
  5. "Ba ni da saurayi a Kannywood — Jamila Nagudu". BBC News Hausa. Retrieved 2022-03-25.
  6. "Opera News Detail". lucky-wap-ams.op-mobile.opera.com. Retrieved 2022-03-25.