Wannan shine jerin asibotoci a Jamhuriyar Nijar. Bankin duniya ya fitar da rahotin cewar a shekarar 2001 akwai asibitoci 40 a Nija, akasarin su kananan asibitoci ne. Akwai ma'aikatan lafiy 296 a fadin kasar mai yawan mutane miliyan 13 a 2004.[1] Anan an kawo jerin manya daga cikin asibitocin.
Gwamnatin turaean mulkin mallaka ce ta kirkire shi a 1922, anbata sunan (Hopital National de Niamey or HNN) a 1962. Asibitin zamani ne wanda gwamanatin kasar ke tagiyar dashi. Shine babban asibiti a kasar wanda ke samar da harkar lafiya mafi girma a kasar. Sauran asibitoci a kasar na aikewa da marasa lafiya Babban asibitin Niamey ko Asibitin Lamordé.